Malami ya fada ma Sanusi: kudirinka a kan Karin aure zai keta dokar Al-Qur’ani

Malami ya fada ma Sanusi: kudirinka a kan Karin aure zai keta dokar Al-Qur’ani

Bayan shirye-shiryen da sarkin Kano, Muhammadu Sanusi keyi na gabatar da dokar da zai hana maza matalauta a masarautar daga auren mata da yawa Aminu Daurawa, shugaban kungiyar Hisbah ta jihar Kano, wani jami’in dan sandan musulunci yace Allah ya bayyana yadda matsayin aure yake a Al-Qur’ani kuma duk wasu ka’idoji zai zama a matsayin “karya doka.”

Malami ya fada ma Sanusi: kudirinka a kan Karin aure zai keta dokar Al-Qur’ani

Jaridar Cable ta ruwaito cewa Daurawa yace abi ka’idojin kara aure kamar yadda bayyane a cikin Al-Qur’ani sosai.

Sannan Daurawa ya shawarci basaraken da ya mayar da hankali gurin wayar ma jama’a kai a kan matsalolin dake cikin tara matan aure da yawa.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi yayi ma kazaman Almajirai wanka a Maiduguri (Kalli hotuna)

A cewar The Cable, Daurawa ya bayyana a wata hira da BBC Hausa a ranar Juma’a, cewa a sanya darasin cikin tsarin karatun makaranatr Sakandare don masu tasowa su san abunda zai fiye masu.

“Allah ya bayyana matsayin aure a cikin Al-Qur’ani mai tsarki kuma duk wani karya doka abun korewa ne,” cewar Daurawa.

“Abunda ya kamata ayi shine wayar da kan mutane kan matsalolin dake cikin tara matan aure da yaw aba wai a sanya dokar da zai hana matalauta auren fiye da mata daya ba.

“Akwai kimanin dokoki 13 da mutun zai bi kafin ya kara aure kuma wannan ya hada da adalci da kuma kulawa ga matar kamar yadda yake a cikin Al-Qur’ani.”

A halin da ake ciki kungiyar kare hakki musulmai (MURIC) ta yaba ma sarkin Kano Muhammadu Sanusi kan shirin gabatar da dokar da zai hana maza talakawa daga auren mata da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel