Wani mugun ciwo ya kara dawowa Najeriya

Wani mugun ciwo ya kara dawowa Najeriya

– Wannan mugun cutar da aka sani na ‘Lassa’ ya dawo gari

– Yanzu haka ya hallaka mutane a Garin Bauchi

– Kwamishinar lafiya ta Jihar ta bayyana haka

Wani mugun ciwo ya kara dawowa Najeriya
Wani mugun ciwo ya kara dawowa Najeriya

‘Lassa’ mugun cutar nan da aka sani ta dawo gari yanzu haka har ta aika wasu bayin Allah Lahira. Kamar dai yadda aka sani dabbobi irin su bera ne ke kawo zazzabin na Lassa.

Kamar yadda muka samu labari daga jaridar Daily Trust, wannan mugun cuta ta dawo Garin Bauchi har kuma tayi sanadiyar mutuwar mutane 4. Kwamishinar lafiya ta Jihar bauchi Dakta Halima Mukaddas ta bayyanawa manema labarai wannan a yau.

KU KARANTA: Ko meyasa Arewa ke fama da talauci?

Dakta Halima tace an samu bullowar cutar ne a Garuruwan Alkeri da Ganjuwa. Kwanakin baya dai wannan zazzabi na lassa ya bullo gari inda yayi sanadiyar rashin rayukan mutane kusan 2 a Bauchi. An dai gargadi Jama’a su guji bera wanda shi ke yada kwayar cutar.

A wani bangare kuma Masana masu hange da binciken Duniya sun bayyana cewa za a samu husufin rana a sassan kasar nan a Ranar Lahadi. Ko da yake dai masanan sun ce abin ba wani mai kamarin gaske bane musamman a Arewacin kasar.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel