Yan Boko Haram sun hallaka soji 7 a wani sabon hari

Yan Boko Haram sun hallaka soji 7 a wani sabon hari

- Yan kungiyar Boko Haram sun kai wata mumunan hari Gajiram, wani gari da ke kusa da birnin Maiduguri

- Sojojin Najeriya 7 ne suka rasa rayukansu a wannan hari

Yan Boko Haram sun hallaka soji 7 a wani sabon hari
Yan Boko Haram sun hallaka soji 7 a wani sabon hari

An bada rahoton cewa wani Laftanan na soji ya rasa rayuwarsa sanadiyar wata harin da Boko Haram ta kai garin Gajiram, wani gari da ke kusa da Maiduguri.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Laftanan din ya rasu ne tare was soji 6 a harin da aka kai musu.

KU KARANTA: Buhari yayi magana da Masari

Wani dan banga mai suna Babakura Kolo yace anyi musayar wuta na tsawon awa 2 tsakanin yan Boko Haram da soji inda soji 3 suka mutu a take.

Bayan harin, a yau Juma’a 24 ga watan Fabrairu, mutuwan sojin yah aura 7.

Amma, wata majiyar soji tace an kashe yan Boko Haram guda 3 a harin yayinda soji ke duban wuraren da suke boye a unguwar.

Kolo yace akwai yiwuwan cewa bangaren Abu Musab Al-Barnawi ne suka kai harin.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel