Gwamna Fayose ma yabi, yace Shugaba Buhari mutumen kirki ne

Gwamna Fayose ma yabi, yace Shugaba Buhari mutumen kirki ne

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose a wani jawabin sa wanda ba kasafai yake irin sa ba ya jinjinawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhai saboda tura sunan Mai shari'a Walter Onnoghen zuwa majalisa don tantacewa.

Gwamna Fayose ma yabi, yace Shugaba Buhari mutumen kirki ne

Gwamna Fayose ma yabi, yace Shugaba Buhari mutumen kirki ne

Shi dai Fayose yayi kaurin sunane wajen caccakar shugaba Buharin da manufofin sa a siyasance amma sai gashi ya fito yana yabon sa a kan cewa lallai Shugaba Biharin yana sauraron kukan yan kasar sa.

KU KARANTA: Na ba alkali kudi amma ba cin hanci bane - Lauyan Buhari

A wani labarin kuma, Labarin da ke iso mana yanzu yana nuni da cewa yan bindigar da suka yi awon gaba da Farfesan nan dan kasar Jamus Peter Breunij da wani abokin sa Johannes Buringer a kauyen Jenjela kusa da garin Kaduna sun kira abokan aikin su inda kuma suka bukaci zunzurutun kudi har N60miliyan.

Su dai yan bindigar kamar yadda bayanai suka tabbatar sun sace turawan ne a cikin karamar hukumar Kagarko inda kuma yanzu haka suke neman a basu N30miliyan a kan kowanen su don su sako su.

A jiya dai wannan kafar labaran ta ruwaito maku cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun hallaka mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutanen guda biyu a jihar Kaduna, dake yankin Arewacin Najeriya.

Jaridar Sahara ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Laraba 22 ga watan Feburairu akan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel