Gaskiya ya bayyana: Lauyan Shugaba Buhari ya nesanta shugaban daga bai wa alkali Kudi

Gaskiya ya bayyana: Lauyan Shugaba Buhari ya nesanta shugaban daga bai wa alkali Kudi

Lauyan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nesanta shugaban daga zargin bai wa wani alkali Adeniyi Ademola kyautar naira 500,000.

Gaskiya ya bayyana: Lauyan Shugaba Buhari ya nesanta shugaban daga bai wa alkali Kudi
Gaskiya ya bayyana: Lauyan Shugaba Buhari ya nesanta shugaban daga bai wa alkali Kudi

Wani shaida da ya bayyana a gaban kotu a shari'ar cin hanci da ake yiwa alkali Ademola ya ce Buhari ya bai wa Lauyan kyautar kudin a dai dai lokacin da alkalin ke sauraron tuhumar da ake yiwa shugaban na rashin mallakar shaidar kammala karatu.

Lauyan Buhari Kola Awodein ya ce daga aljihun sa ya bai wa mai shari'a Ademola kudin a matsayin gudumawar auran 'yar sa da aka yi a Legas.

KU KARANTA KUMA: Koshin lafiyan Buhari:Manyan yan siyasa 8 da sun yi shiru

Awodeyin ya ce ba da sanin Buhari ya yi kyautar ba kuma babu hannun shugaban a ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel