Dalilin da yasa Arewa tafi kowani yanki talauci – Sanata Shehu Sani

Dalilin da yasa Arewa tafi kowani yanki talauci – Sanata Shehu Sani

Sanata mai wakiltar Kaduna tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani, ya dauran laifin cigaban talaucin arewa akan yan siyasan arewacin Najeriya.

Dalilin da yasa Arewa tafi kowani yanki talauci – Sanata Shehu Sani
Dalilin da yasa Arewa tafi kowani yanki talauci – Sanata Shehu Sani

Game da cewarsa, arewa ce yanki amfi talauci a Najeria duk da cewa tanada masu hannu da shuni a yankin.

Sani yace : "Talakawa nayi mana aiki, domin suka cewa mun samu nasara a zabe, amma babu riba.

“Koda yaushe batun daya ne; du lokacin da muke neman yin takara a zabe, muna nemansu lungu da tsako, amma idan muka samu nasara, sai muyi watsi da su.

KU KARANTA: Ana yiwa Buhari ruwan addu'o'i

“Ba aka iya hana bara a ko ina na kasan nan ba idan baka bunkasa rayuwan mutane ba. Matsalan kenan.

“Bara ta zama wani babban mastala da muke fama da shi a arewacin Najeriya amma ba za’a iya hanawa ba saboda ba’a magance matsalan tattalin arziki ba.

“Yan arewa masu arziki da dama, wadanda sun mallaki rijiyoyin mai kuma suna zaune a manyan kujeru, suna kallon wadannan mutane a matsayin wadanda ya kamata a share, amma ba za’a iya sharesu ba.

“Munada masu kudi da dama a arewa wadanda zasu iya kawar da wannan bu.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel