Wai shin menene gaskiyar dalilin cigaba da zaman Buhari a Landan?

Wai shin menene gaskiyar dalilin cigaba da zaman Buhari a Landan?

Da alamu dai za’a fara wani sabon wasan kwaikwayo na ‘Big Brother’ a Najeriya biyo bayan cigaba da zama a birnin Landan da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ke yi.

Wai shin menene gaskiyar dalilin cigaba da zaman Buhari a Landan?
Buhari a Landan?

Kai ku tsaya, ba’a nake, ya ma za’a yi ace babban janar mai murabus zai shirya wasan kwaikwayo? Amma fa akwai kamaceceniya tsakanin wasan kwaikwayon da tafiyar shugaban kasar, tunda dai dukkaninsu ba a Najeriya ake yin su ba.

Bambamcin kawai, shaukin wasan Big Brother ya ragu matuka, amma cece kucen da tafiyar shugaba Buhari ta janyo na cigaba da karuwa, tafiyar shugaba Buhari ta zo ne daidai lokacin da giwar Afirka take fama da karayar tattalin arziki, da kuma barazanar fari dake neman mamaye yankin Arewa maso gabas din dake fama da yan ta’addan Boko Haram.

Wani bambamcin dake tsakanin Big Brother da tafiyar Buhari shine, yayin da ake samun cikakken bayanai akai akai dangane da Big Brother, ba’a samun wani muhimmin labara dangane da shugaba Buhari, sai dai hotunansa kawai da yan Najeriya suke gani a Facebook da Tuwita.

KU KARANTA: Aci shiru: Yan siyasa 7 da basu ce uffan ba game da rashin lafiyar shugaba Buhari

Kwanan na ma yayi magana ta bakin Kaakakinsa, wanda yace ai shugaban na nan lafiya lau, kada mutane su damu, hutu kawia yake samu. Sai dai tafiyar na shugaban ya harzuka yan Najeriya, bayan suna sane da alkawarin da shugaba Buhari yayi na rage fice ficen yan najeriya zuwa asibitocin kasashen waje ta hanyar inganta asibitocin kasar.

Ko a watan Yuni daya gabata, shugaban kasa Buhari ya shafe satuka 2 a birnin Landan, inda aka duba lafiyar kunnensa, kuma dai har yanzu ba’a sanar da yan Najeriya ciwon dake damun shugaban ba, da kuma yaushe ne zai dawo Najeriya.

Matakan daya kamata a dauka

Duk da maganganun da aka samu daga bakunan mashawartan shugaban kasar dangane da lafiyar shugaban, yan Najeriya basu daina watsa jita jita ba dangane da lafiyar tasa, saboda suna tuna halin da

kasar ta shiga ne bayan tafiyar Umaru Musa Yar’adua asibiti a shekarar 2010, inda a can ne ya rasu.

Shima haka aka kwashe watannin ba tare da sanar da yan Najeriya halin dayake ciki ba yayin dayake samun kulawa a kasar Saudiyya, daga nan ne fa kasar ta shiga rudani.

Amma magoya bayan shugaba Buhari sunce a daina kwatanta Yar’adua da Buhari, inda suke cewa shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Osinbajo, yayin da shi kuma Yar’adua bai mika ma mataimakinsa a wancan lokaci Jonathan mulki ba, sa’annan shugaba Buhari yayi waya da mutane da dama ciki har da shugaban kasar Amurka, yayin da Yar’adua kuwa babu wanda ya jiyo muryarsa.

Masanin al’amuran siyasa Farfesa Jibrin Ibrahim yace “shugaba Buhari yayi abinda tsarin mulkin kasa ya tanadar masa, don haka bai nuna yunwan mulki ba kamar yadda shuwagabannin Afirka suke yi.”

Wai shin menene gaskiyar dalilin cigaba da zaman Buhari a Landan?

Farfesa ya cigaba da fadin:

“Damuwata itace gwamnatin tana ganin kamar tana da wani lokaci mai tsawo, musamman wajen gyaran tattalin arzikin kasa, bayan sauranta shekaru kadan. Sai dai tabbas a rashin shugaba Buhari, Farfesa Osinbajo ya nuna kwazo da jarumta ta yadda yake gudanar da shugabanci yadda ya kamata

“Kaga ya shiga har cikin yankin Neja Delta don bayyana musu tarin tagomashi da gwamnati ta tanadar musu, sa’annan ya samu ganawa da tsagerun yankin don yin sulhu musamman hana su fasa butun mai.”

Sai dai duk da wannan, magauta na fadin ai mukaddashin shugaban kasar ba shi da cikakkeb iko.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel