Bututun mai ya kama da wuta a Port Harcourt

Bututun mai ya kama da wuta a Port Harcourt

Wani bututun mai mallakar kamfanin Nigeria Liquefied Natural Gas (NLNG) ya kama da wuta wanda hakan ne ya haddasa tashin hankula a tsakanin mazauna gurin.

A wata sanarwa daga NLNG a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu, yace har yanzu ba’a san abunda ya haddasa tashin wutan ba amma ya ba da tabbacin cewa babu wanda ya hallaka.

KU KARANTA KUMA: Wadanda ke kewaye da Buhari zasu hallaka Najeriya – Junaid Mohammed

Ga yadda jawabin yazo: “Gobara ya afku a yammacin ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu 2017 a sashin wasu bututunan mai guda biyu, wanda daya daga ciki mallakar kamfanin NLNG ne, kimanin kilomita 3 daga Rumuji a jihar Rivers.

“Har yanzu ba’a san abunda ya haddasa al’amarin ba. Ba’a rahoto cewa wani yaji ciwo ko kuma ace an rasa rai ba. A take aka kawo hukumar bada agajin gaggawa da sauran hukumomin da ya kamata. An shawarci garuruwan dake kusa da inda al’amarin ya faru da cewan karda su tunkari gurin don tsirar da rayuwarsu.

“An kuma dauki duk wani mataki da ya dace don tabbatar da cewan al’amarin bai yi tsauri ba. A halin yanzu, ana bincike cikin al’amarin.”

Jaridar Sun ta ruwaito cewa akwai rade-radin cewa gobarar ya tashine sakamakon zafi ko kuma yan bindiga.

KU KARANTA KUMA: Duk wanda ya ce na nemi shugabancin kasa yanzu ya na da tabuwan hankali – Kashim Shettima

Cif Ndudirim Amadi yace: “Ban san abunda ya haddasa gobaran ba, amma ina tunanin zafi yayi yawa ne a kan bututun; shiyasa ya tashi. Wannan ya haddasa tsoro a garinmu. Tunkudin da danyen man keyi daga bututun, ya haddasa girgizan kasa a ko ina.”

Ya kuma yi ikirarin cewa ya hallaka amfanin gona a yankin.

Yankin sun fuskanci tashe-tashen bututun mai a baya daga yan bindiga koda dai abun ya lafa a yanzu tunda aka fara tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da shugabanni daga yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel