Osinbajo dan halal ne Inji ‘Yan Neja-Delta

Osinbajo dan halal ne Inji ‘Yan Neja-Delta

– Mukaddashin shugaban kasa ya sha yabo daga tsofaffin tsagerun Neja-Delta

– Tsofaffin tsagerun suka ce Osinbajo dan halal ne

– An dai yabawa yadda Osinbajo ke tafiyar da sha’anin kasar

Osinbajo dan halal ne Inji ‘Yan Neja-Delta
Osinbajo dan halal ne Inji ‘Yan Neja-Delta

Kungiyar wasu tubabbun tsagerun Neja-Delta sun yabawa Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da irin yadda yake jagorantar kasar tun bayan da ya karbi ragamar. Kusan wata guda kenan yanzu da mika masa madafan iko.

Kungiyar ta Neja-Delta tace shugaban kasar na rikon kwarya ya nuna dattaku da sanin ya kamata, sannan kuma ya nuna amana ga mai gidan sa shugaba Muhammadu Buhari. Kungiyar ta yabawa Osinbajo tace akwai abin koyo a gare sa.

KU KARANTA: Kayan abinci sun shigo Najeriya

Shugaban wannan kungiya Eshanekpe Israel Akpodoro ya bayyanawa Legit.ng yana goyon gwamnatin shugaba Buhari ya kuma ce Mataimaki Osinbajo bai zo da cin amana ba. Kusan wata guda kenan da shugaba Buhari ya mikawa Osinbajo mulki ya tafi Birnin Landan.

Jiya ne Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya saki kudin wasu manyan kwangiloli. Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar ginin titin kan iyaka tsakanin Najeriya da kasar Kamaru da kuma wani babban titi a gabashin kaduna mai kilomita 15. Ana kuma shirin fara aikin babban gadar Neja-Delta.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel