Manyan jiragen ruwa guda 29 sun nufo Najeriya makare da mai, da kayayyakin abinci

Manyan jiragen ruwa guda 29 sun nufo Najeriya makare da mai, da kayayyakin abinci

Kimanin manyan jiragen ruwa guda 29 ne suke gab da tashar jiragen ruwa dake jihar Legas makare tam da kayayyakin abinci a ranar don sauke su daga ranar 22 ga watan Feburairu zuwa 6 ga watan Maris.

Manyan jiragen ruwa guda 29 sun nufo Najeriya makare da mai, da kayayyakin abinci
Manyan jiragen ruwa guda 29 sun nufo Najeriya makare da mai, da kayayyakin abinci

Hukumar kula da tashashen ruwa, NPA ne ta bayyana haka a ranar Laraba a jihar Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta ruwaito, NAN.

KU KARANTA: 'Ɓatar dabon naira miliyan 500: babban akanta na ƙasa ya gurfana gaban ýan majalisu

Rahotannin sun bayyana cewar shidda daga cikin jiragen zasu sauke man fetur, yayin da daya kuma zai sauke iskar gas. NPA tace sauran jirage 22 kuwa suna dauke ne da garin fulawa, siga, karafa, taki da dai saurana kayayyakin masarufi.

Rahoton ya cigaba da bayyana cewar a yanzu haka akwai jirage guda 6 dake sauraren samun umarnin sauke kayayyakin su don sauke man fetur da takin zamani, sa’annan wasu jirage 14 kuma suna sauke sundukai, waken soya, gishiri da man iskar gas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel