Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam

Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam

- Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta gano wasu manyan motoci goma sha bakwai

- An gano motocin ne a wani gidan gona dake mallakar tsohon shugaban hukumar Kwastam, Abdullahi Dikko Inde

- Gidan gonar ya kasance a unguwar Nnamdi Azikwe dake jihar Kaduna

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC ta gano wasu motoci guda goma sha bakwai 17 daga tsohon shugaban hukumar kwastam, Abdullahi Dikko Inde.

Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam

An gano motocin ne a wani gidan gonan dake kan layin Nmandi Azikwe dake jihar kaduna.

Hukumar tace taje binciken wasu kudade ne, akan wani rahoto da suka samu daga jihar kano akan cewa ana zargin akwai wasu kudade da aka boye a unguwar acikin wannan gidan gona.

KU KARANTA KUMA: Wadanda ke kewaye da Buhari zasu hallaka Najeriya – Junaid Mohammed

Hukumar ta EFCC ta kara da cewa alokacin da take gudanar da bincike ne taci karo da wadannan motoci har guda sha bakwai 17,wanda alamu sun nuna cewa babu motar da aka taba hawa acikin su kuma manyan motoci ne.

Sannan bincike ya tabbatar da cewa wadannan motoci na Abdullahi Dikko Inde ne, inda tasamu cikakken bayani daga mutanen unguwar da suka bada tabbacin cewa motocin mallakar tsohon shugabar kwastan na kasa ne.

Ga hotunan sauran motocin da aka gano a kasa:

Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam
Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam
Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam
Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam
Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam
Hukumar EFCC ta kwato motoci 17 daga tsohon shugaban hukumar Kwastam

Asali: Legit.ng

Online view pixel