Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi

Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi

Yayin yakin neman zaben shugabancin kasar nan a shekara 2015, wata rikici ta taso haikan kan sahihancin takardar sakandaren shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a lokacin yake takara a karkashin jam’iyyar APC.

Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi
Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi

A wancan lokaci, jam’iyya mai mulki PDP ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa ba shi da shaidar kammala karatun sakandari, wanda shine ka’idar shiga takarar shugaban kasa a Najeriya.

Amma daga bisani, hukumar soji sun gano shaidar kammala sakandaren shugaba Buhari. Sai dai a yan kwankin nan an sake tada rikita rikitan takardar shaida shugaban kasar, yayin da wani shaida a shari’a alkali Ademola Adeniyi, yana fadin cewa shugaba Buhari ya baiwa alkali Ademola cin hancin N500, 000 a lokacin da yake sauraron karar takardar shaidar shugaban kasar.

Legit.ng ta samo muku sahihan hotuna guda biyar da suka tabbatar da shugaba Buhari yayi karatu sosai sosai.

1. Shugaba Buhari ya halarci makarantar sakandari ta Katsina Middle School daga shekarar 1948 zuwa 1952, daga nan ya wuce makarantar sakandari ta Katsina Provincial secondary school daga 1956 zuwa 1961.

Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi
Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi

Daga nan ne kuma ya wuce makarantar horon sojoji.

2. Shugaban kasa Buhari ya garzaya makarantar horon sojoji dake Mons Officer Cadet School, dake garin Aldershot kasar Birtani a shekarar 1962 – 1963. Shima janar Olusegun Obasanjo tare da Sani Abacha duk sun halarci kwalejin horon. A wannan kwalejin ne mahukuntar makarantar suka yaba ma Buhari inda suka ce “Buhari wani tauraro ne cikin taurari, kuma mai natsuwa tare da Ankara sosai.”

Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi
Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi

3. A shekarar 1962 ne shugaba Buhari ya zama cikakken soja, inda ya taka matakalai na mukamai daban daban, kuma a shekarar ne ya koma makarantar horar da hafsan soja.

Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi
Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi

KU KARANTA: ‘Sakataren gwamnati Babachir ba miciyin amanar Buhari bane’ – inji wata Ƙungiya

4. Bugu da kari, shugaba Buhari ya halarci cibiyar ayyukan tsaro na gwamnatin kasar Indiya dake garin Wellington, inda ya kammala karatunsa a wannan cibiya a shekarar 1973.

Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi
Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi

5. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da karatunsa a kwalejin yaki na kasar Amurka tsakanin shekarun 1979 zuwa 1980, inda mahukuntan kwalejin suka bayyana Buhari a matsayin “cikakken mutum, kuma soja mai sanyin magana wanda baya wasa da ka’idojin aikin soji”

Hotunan sakandaren da shugaba Buhari ya halarta, tare da sauran makarantun da yayi
Hotunan shugaba Buhari tare da yan ajinsu a Amurka

Mahukuntan sun cigaba da cewa “yana girmama mata tare da ganin mutuncinsu musamman idan zai gaishe su ta hanyar sanya hannunsa kan hularsa, kuma baya shiga daki da tare da ya cire hularsa ba, kuma yana tauna magana kafin ya furta, ga shi mai yawan murmushi sa’annan ba zai taba yin abinda zai kawo matsala ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel