Muna goyon bayan sarkin Kano Sanusi akan kafa dokar kara aure – Kungiyar MURIC

Muna goyon bayan sarkin Kano Sanusi akan kafa dokar kara aure – Kungiyar MURIC

Kungiyar kare hakkin musulmai wato Muslim Rights Concern (MURIC) ta nuna goyon bayanta kan kiran da sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu yayi na kirkiro wata doka da zai hana duk wani na miji kara aure ba tare da ya cika wadansu sharudda ba kamar yadda addinin musulunci ya koyar.

Muna goyon bayan sarkin Kano Sanusi akan kafa dokar kara aure – Kungiyar MURIC

Sarkin Kano Sanusi ya yi kira da kafa wata doka da zai rage yadda maza ke kara aure yadda suka ga dama ba tare da bin ka’idojin da addinin musulunci ya shimfida ba saboda kawai sun maida yin hakan wani abin jin dadi.

Daraktan kungiyar Ishaq Akintola yace tabbass wannan kira ya yi daidai domin haka ne koyarwar addini da Al-Qur’ani mai girma.

KU KARANTA KUMA: Sarki Sanusi na shirin sanya dokar hana maza matalauta auren mata da yawa

Ishaq ya bayyana hakan ne a garin Ibadan.Ya ce kamar yadda bincike ya nuna, a zahiri mata sun fi maza yawa haka kuma Al-Qur’ani mai girma ya ba namiji ikon iya auren mata 4 domin rage yawan mata wadanda basu da aure amma bai ce kuma ayi yadda zai zamo mana masifa a rayuwar ma’auratan da kasa ba.

Ya kara da cewa Al-Qur’ani mai girma ya umurci namiji ya yi aure idan yana da abin da zai iya rike matan sa kuma zai iya kara wa idan yana da halin iya kula da su duka, sannan yayi adalci a tsakaninsu.

Daga karshe ya yabawa gwamnatin jihar Kano game da dokar da suke kokarin kafawa domin hakan kadai ne zai iya kare maza daga fadawa cikin matsalar auren matan da baza su iya kula da su ba da kuma haifo ‘ya’yan da ba za su iya kula da su ba inda daga karshe su zamo bata gari da yan iska.

Asali: Legit.ng

Online view pixel