Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff

Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff

Shugaban jam’iyyar PDP wanda kotu ta tabbatar Ali Modu Sheriff ya samu wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Litinin 20 ga watan Feburairu.

Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff
Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff

Jigajigan yan siyasan sun gana ne a gidan tsohon shugaban kasa mai girma Goodluck Jonathan inda suka sahe awanni da dama suna tattaunawa jim kada bayan jami’an tsaro sun fatattaki PDP bangaren Makarfi daga gudanar da taron masu ruwa da tsaki a katafaren dakin taro na kasa, International Conference Centre.

KU KARANTA: Rikicin PDP: Jonathan ya goyi bayan Sheriff a matsayin shugaba

Jaridar The Nation ta ruwaito Sheriff ya isa gidan tsohon shugaban kasa Jonathan ne da misalin karfe 4:25 na safe, inda ya samu rakiyar wasu shugabannin jam’iyyar ba bangarensa, ciki har da mataimakin shugaban jam’iyya Dakta Cairo Ojougboh, sakataren jam’iyya Farfesa Wale Oladipo da sakataren kudi Adewole Adeyanju.

Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff

Haka zalika an hangi keyar Ahmed Gulak, tsohon mai baiwa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa, da tsohon minista Yerima Ngama, da Sanata Umar Gada duk a cikin wadanda suka take ma Modu Sheriff baya zuwa gidan Jonathan.

Yayin dayake yi ma yan jaridu jawabi bayan ganawar, Jonathan yace “bamu da wani bangare a jam’iyyar mu, dukkanin mu abu daya ne, na gana da Sheriff, kuma na gana da sauran. Bama son rarrabuwar kai a jam’iyyar mu.”

Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff
Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff

Shima Sheriff yace “PDP daya muke da shi, shugaba ma daya ne, kuma muna yin kokarin saita komai don ganin mun hada kan jam’iyyar.”

Rikita rikitan PDP: Goodluck Jonathan yayi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff

Da fari, shima kaakakin bangaren Makarfi Yarima Dayo Adeyeye ya zargi Sheriff da hada kai da APC don su karya lagon jam’iyyar PDP.

Sai dai bayan jami’an tsaro sun fatattaki Makarfi da ahalinsa daga babba dakin taro na ICC sai suka zarce gidan gwamnatin jihar Ekiti dake Abuja, a can suka yi nasu taron. Ga bidiyon ganawar Jonathan da Makarfi a satin daya gabata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel