'Yan sanda sun damke wasu barayin yara su 2 a Kano

'Yan sanda sun damke wasu barayin yara su 2 a Kano

-Dubun wani saurayi da budurwa da suka saci wani karamin yaro a Kano ta cika yayin da suka fada hannun 'yan sanda

-Barayin sun yi nasarar sace yaron da kuma garkuwa da shi tare da neman fansa na naira miliyan guda daya kafin su sake shi.

'Yan sanda sun damke wasu barayin yara su 2 a Kano
'Zanga-zangar wasu mata kan yawaitar satar yara a Kano

Wannan lamari ya faru ne a barayin yaro ta cika a Kano yayin da suka sace wani karamin

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta yi holin wasu mutane 2 da ake zargi da satar wani karamin yaro tare da garkuwa da shi da kuma neman kudin fansa na Naira miliyan 1.

Rundunar 'yan sandan a wani taron manema labarai a shalkwatarta a ranar Litinin 20 ga watan Fabarairun 2017 a shalkwatar ta da ke unguwar Bompai, ta inda ta kuma gabatar da wadanda ake zargin su biyu ga manema labarai.

A cewar Kakakin rundunar ASP Musa Majiya, wadanada ake zargi su biyu Abubakar Bushasha da kuma Hafsat Auwal Hotoro sun saci wani karmin yaro ne wanda ba bayyaana sunansa ba a unguwar Ladanai tare da yin garkuwa da hsi da kuma nema fansa na Naira mliyan 1.

Wanda ake zargi Abubakar Bushasha amsa zargin da ake yi tare da karin bayanin yadda suka kitsa sace yaron da kuma dalilinsu na yin haka watau neman biyan bukata ta kudi da budurwar tasa ta matsa ta na so daga hannunsa.

Ita ma Hafsat ta amzsa zargin tare da bayar da bayanin yadda suka sace yaron ta hanyar shiga wani gida da ta yi, da kuma nemi a ba ta yaron da suna zai raka ta wani gida ne, daga bisani suka gudu da shi, tare da yin garkuwa da kuma neman kudin fansa har na milyan guda daga wurin iyayensa.

'Yan sanda sun samu nasarar cafke su ne bayan ta hanyar asusun ajiyar bankin da suka bayar domin a sa musu kudin a cewar wani rahoton gidan Rediyo mai zaman kansa a jihar.

Nasarar kama wannan barayi ya zo nne a lokacin da wasu mata suka fito zanga-zanga a rmakon jiya kana yawaitar satar yaran musamman a unguwanni Hotoro da Kawo Lambu da Walalamae da kuma Ladanai a inda masu zanga-zangar suka je gidan gwamna da kuma Fadaar mai marataba sarkin Kano.

Hukumomi a Kano na cigaba da kira ga iyaye da su kara sa ido a kan yaransu da kuma bakuwar fuska a unguwanni su.

Ra'ayin jama kan salon mulkin Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel