Shugaban kasa Osinbajo yayi alkawari ya saba

Shugaban kasa Osinbajo yayi alkawari ya saba

– Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo yayi alkawari ya gaza cikawa

– Osinbajo yayi alkawarin zuwa Jihar Ondo sai dai bai samu zuwa ba

– Shugaban kasar na rikon-kwarya ya bada uzurin sa

Shugaban kasa Osinbajo yayi alkawari ya saba
Shugaban kasa Osinbajo yayi alkawari ya saba

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi alkawarin zuwa Jihar Ondo kai ziyara sai dai har yanzu ya gaza cikawa. Tun kwanaki dai Osinbajo yake sa ranar zuwa Jihar Ondo amma abin ya faskara.

Mai magana a madadin sa Laolu Akande yace yanayi ne na hazo ya hana Mukaddashin shugaban kasar tashi a jirgi. Shugaban kasar na rikon-kwarya Osinbajo ya ba mutanen Akure da ma Jihar baki daya hakuri bayan ya fasa tafiyar.

KU KARANTA: Mutanen Katsina na tayi wa Buhari addu'a

A Ranar Litinin dinnan ne dai Farfesa Osinbajo yayi niyyar zuwa Birnin Akure ya kai ziyara Garin Gwamna Mimiko wanda ke shirin sauka daga mulki. Kwanakin nan dai Osinbajo ya kai ziyara Garuruwan da ke Kudancin kasar na Ribas, da Bayelsa da kuma Imo.

Haka dai kwanaki shugaba Muhammadu Buhari ya gaza zuwa Jihar Bauchi. Yanzu haka dai Farfesa Yemi Osinbajo ke rike da kasar, kuma Jama’a da dama har ‘yan adawar shugaba Muhammadu Buhari suna yabawa aikin Mukaddashin shugaban kasar. Wasu har suke cewa Buhari yayi zaman sa ya huta.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Osinbajo ya gargadi Malaman Addini

Asali: Legit.ng

Online view pixel