Farin jinin Jami'ar Maiduguri duk da tashe-tashen bama-bamai

Farin jinin Jami'ar Maiduguri duk da tashe-tashen bama-bamai

-Duk da tashe-tashen bama-bamai a Maiduguri da kuma jamai'ar a kwanan nan jami'ar, har yanzu dalibai na tururuwa zuwa jami'ar.

-Neman gurbin karatu na zangon karatun 2016/2017 ya kasance daban saboda yawan wadanda su ka nema ya kai 46,000 ba kamar lokacin da tada kayar baya ya yi kamari ba inda yawan bai wuce 3000 ba.

Farin jinin Jami'ar Maiduguri duk da tashe-tashen bama-bamai
Farin jinin Jami'ar Maiduguri duk da tashe-tashen bama-bamai

A safiyar ranar Litinin ne 16 ga watan Janairu 2017 wani bam ya fashe a masallacin jami'ar Maiduguri a jihar Borno.

Wasu dalibai da ma'aikata sun je masallacin don sallar Asuba lokacin da bam din ya tashi.

Wannan ba shi ne karon farko da bam ya tashi a Maiduguri ba, duk da haka har yanzu Jami'ar Maiduguri na daya daga cikin jami'o'in da aka fi nema a Najeriya.

Kasancewarta jami'a ta farko a yankin Arewa maso Gabas ya ba ta damar samun ingancin karatu a ciki da wajen Najeriya. Ingancin karatun jami'ar na daya daga cikin dalilan da su ka sa ake ci gaba da tururuwa zuwa neman ilimi.

Neman gurbin karatu na zangon karatun 2016/2017 ya kasance daban saboda yawan wadanda su ka nema ya kai 46,000 ba kamar lokacin da tada kayar baya ya yi kamari ba inda yawan bai wuce 3000 ba.

A cikin 46, 000 da su ka nema, sama da 7000 sun samu, adadin da jami'ar Ilori ce kadai ke iya dauka a arewa.

Akwai manyan shahararrun mutane da su ka yi karatu a jami'ar, wadanda su ka hada da:

Tsohon gwamnan jihar Abia Dr. Orji Uzo Kalu da gwamna mai ci Victor Ekpaezu. Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello, wanda ya karanta fannin tsimi da tanadi.

Haka ma tsohon ministan babban birnin tarayya lokacin mulkin Jonathan, Bala Muhammad ya kammala karatunsa a sashin nazarin harshen Turanci na jami'ar.

Sarkin Gombe na yanzu, Abubakar Shehu Abubakar, shi ma ya karanta fannin jagoranci a jami'ar.

Gwamnatin mulkin soja ta Yakubu Gowon ce ta kirkiri jami'ar tare da wasu jami'o'i shida a shekarar 1975 da niyyar bunkasa ilimin gaba da sakandare a kasa. Jami'o'in su hada da:

Jami'ar Fatakwal da Jami'ar Calabar da Jami'ar Usmanu Danfodio, Sakkwato da Jami'ar Bayero ta Kano da kuma Jami'ar Jos, wadanda ake bayyanawa da jami'o'in zamani na biyu.

Ga hoton bidiyon zanga-zangar goyon bayan shugaba Buhari da aka yi a kwanan nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel