Kwamitin ladabtarwar APC ta aika ma Kwankwaso takardar sammaci

Kwamitin ladabtarwar APC ta aika ma Kwankwaso takardar sammaci

Kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta aika ma tsohon gwamnan jihar kuma jigo a jam’iyyar APC Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso sammaci daya gurfana a gabanta a ranar 3 ga watan Maris.

Kwamitin ladabtarwar APC ta aika ma Kwankwaso takardar sammaci
Kwamitin ladabtarwar APC ta aika ma Kwankwaso takardar sammaci
Asali: Depositphotos

Takardar sammacin mai dauke da kwanan wata 19 ga watan Feburairu ta samu sa hannun shugaban kwamitin ladabtarwar Muhamamd Nadu Yahaya ta bukaci Kwankwaso daya tabbata ya gurfana a gaban ta a babban ofishin jam’iyyar dake kan titin hanyar Maiduguri, birnin Kano.

KU KARANTA: Yadda Andrew Yakubu ya shirya kawar da El-Rufa’i da kudaden sata a zaben 2019

Cikin wasikar sammacin, wanda jaridar Daily Trust tayi arba da ita, kwamitin ta bukaci Kwankwaso da yazo ya tsibe mata bayani dangane da zargin cewa magoya bayansa sunyi kokarin kutsa kai cikin gidan gwamnatin jihar Katsina yayin da ake gudanar da taron jam’iiay APC na yankin Arewa maso yamma a gidan gwamnatin.

Wasikar tace “kwamitin na gayyatar Sanata Kwankwaso ne don ya tsatstsage mata bayani kan dalilin daya sanya shi shirya gangamin siyasa a jihar Katsina a ranar 29 ga watan Janairu an 2017, daidai lokacin da shuwagabannin APC yankin Arewa maso Yamma ke gudanar da taro.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel