TA’ADDANCI: Shettima da jami’in tsaro sun gana yadda za a murkushe Boko Haram

TA’ADDANCI: Shettima da jami’in tsaro sun gana yadda za a murkushe Boko Haram

- Gwamna jihar Borno, Kashim Shettima ya gana da shugabanin sojojin kasa domin samar da sabuwar hanyar durkushe sauran ‘yan Boko Haram a yankin.

- Gwamnan ya yi alkawarin samar da karin motocin sintiri ga jami’in tsaro a fadin jihar.

TA’ADDANCI: Shettima da jami’in tsaro sun gana yadda za a murkushe Boko Haram
TA’ADDANCI: Shettima da jami’in tsaro sun gana yadda za a murkushe Boko Haram

Bayan hare-haren da sauran 'yan Boko Haram ta kai a wasu sassa Jihar Borno, gwamna Kashim Shettima da shugabannin rundunar sojojin Najeriya , ' yan sanda da kuma Sashen DSS sun gudanar da wata ganawa ta gaggawa a makon da ta gabata da nufin daukar sabon matakan da kuma ƙara lura domin dakatar da ‘yan ta’adda a yankin.

KU KARANTA KUMA: Harin kunar bakin-wake ya kashe mutum 19

Kafin ganawa da shugabanin, gwamna Shettima ya gana da Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Leo Irabor na sahohi awa uku a officin gwamna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. A lokacin tattaunawa an sanar da gwamnan takaitacce akan hare-haren na gwanan nan da kuma kokarin da jami’in sojoji ke yi na ganin cewa an durkushe ‘yan ta’adda gaba daya, bisa da wannan ya sa ‘yan Boko Haram ke tayar da kayar baya kasance an raba su da tsohon hedkwatar a dajin Sambisa.

Mai ba gwamna Shettima shawara musamma a kan sadarwa da dabaru , Malam Isa Gusau, ya ce a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 19 ga watan Farairu, cewa bayan ganawa da Kwamandan wanda ba memba na mashawartar tsaro jihar ba, Shettima ya shugabanci taron gaggawar wanda ya samu halartar shugabanin sojojin kasar.

A karshen taron, an kara kafa sabuwar wuraren tsaro a wasu hanyoyi a fadin jihar don dakile motsi sauran ‘yan Boko Haram. An kara girke jami'an tsaro a wurare daban-daban da aka kara da kuma membobi na JTF (matasa yan zaman kai masu hagaza wa jami’in tsaro), yayin da gwamnan ya ba da umurni kara motocin sintiri ga hukumomin tsaro don kara lura da yankin.

Gwamnan ya amince zai ba da wasu taimako domin hagaza ga kokarin gwamnatin tarayya ta karfafa sojojin yayin da za samar da matakan don karfafa wa JTF da kuma mafarauci .

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel