Sarki Sanusi na shirin sanya dokar hana maza matalauta auren mata da yawa

Sarki Sanusi na shirin sanya dokar hana maza matalauta auren mata da yawa

- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi yace zai gabatar da wani doka da zai hana maza matalauta a masarautarsa daga auren mata da yawa

- Sanusi yace ya kulla alaka tsakanin auran mata da yawa, talauci da kuma ta’addanci

- Yace zai tabbatar da cewa ya mika dokar ga gwamnatin jihar don dakatar da yunkurin maza wadanda bazasu iya daukar nauyin mata da yawa ba

Sarki Sanusi na shirin sanya dokar hana maza matalauta auren mata da yawa

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi yace zai gabatar da wani doka da zai hana maza matalauta a masarautarsa daga auren mata da yawa.

Da yake magana a ranar Lahadi gurin taron tunawa da mutuwar Isa Wali, wani tsohon jakadan Ghana karo na 50, Sanusi yace ya alakanta tsakanin auren mata da yawa, talauci da kuma ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: Bana daga cikin makiran Aso Rock – El-Rufai

Yace zai tabbatar da cewa ya mika dokar ga gwamnatin jihar don dakatar da yunkurin maza wadanda bazasu iya daukar nauyin mata da yawa ba

Sanusi: “Mu da muke Arewa mun ga dukkan matsalolin tattalin arziki kan mazaje wadanda basa iya kula da mace daya, da auran mata hudu. Daga karshe sai kuga sun haifi yara 20, ba tare da basu ilimi ba, sais u barsu kara zube a unguwanni, kuma daga karshe sai ku ga sun yan iska da yan ta’adda.

Don haka ya zama sadaukarwa ga Mallam Isa cewa yau, yayinda nake magana, a masarautar Kano wani kwamitin malamai,wanda ni na kafa kuma yake aiki kimanin shekara daya, ta son kawo karshen shawara kan wani dokar iyali da muke shirin gabatarwa a Kano wanda zai magance wasu al’amuran da Mallam Isa ya damu dasu,” cewar Sanusi.

Sanusi yace dokar zai yi jawabin ainahin matsayin Musulunci a kan aure; zai kuma hana auren dole da kuma haramta rikicin cikin gida.

Ya kuma ce zasu shimfida wasu dokoki da sai mutun ya cika su kafin ya auri mata ta biyu da kuma nuna hakkin da ta’allaka a wuyan uba wanda yafi haihafan yara kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel