Yadda Andrew Yakubu ya shirya kawar da El-Rufa’i da kudaden sata a zaben 2019

Yadda Andrew Yakubu ya shirya kawar da El-Rufa’i da kudaden sata a zaben 2019

Wasu labarai da majiya daban daban sun tabbatar da cewar kamammen tsohon shugaban hukumar matatar man fetur ta kasa Andrew Yakubu ya kammala shirye shiryen kawar da gwamnan jihar Kaduna Nasur El-Rufai daga mukaminsa a zabukan 2019 amma fata hanyar amfani da kudaden daya sato daga NNPC, wanda yanzu haka EFCC ta kwace daga hannunsa.

Yadda Andrew Yakubu ya shirya kawar da El-Rufa’i da kudaden sata a zaben 2019

Shi dai Andrew Yakubu yayi kaurin suna ne tun bayan da hukumar EFCC ta bankado wasu makudan kudade a daya daga cikin gidajensa dake layin Kagarko, unguwar sabon tasha garin Kaduna, inda aka gani kimanin dala miliyan 9.8 kwatankwacin naira biliyan 4 kenan.

KU KARANTA: Buhari ya sha alwashin ganin bayan cin hanci da rashawa a Najeriya

Jaridar Sun ta gano cewar Yakubu yana shirin amfani da kudaden ne wajen yakin neman tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a zabukan 2019, don kada Nasir El-Rufai

Rahotanni sun nuna cewar Yakubu ya fara tattaunawa da wata jam’iyya da bat agama samun rajista da hukumar zabe ba don yin takarar tasa, wani makusanci ga Yakubu ya shaida ma jaridar cewar:

“A dai san yana muradin takarar gwamnan jihar Kaduna a 2019, ba sanata ba kamar yadda wasu ke yayatawa ba.”

Wani babban jami’in NNPC yace ba abin mamaki bane yadda Yakubu ya samu wadannan makudan kudade duba da mukamin daya rike a hukumar NNPC, amma abin mamakin shine inda ake je aka boye kudaden.

Wata majiya ta kara da cewa “yana can kasar Amurka yayin daya samu labarin bankado kudaden, amma sai ya dawo gida, inda ya kai kansa ofishin EFCC dake Kano, kuma ya cika dukkanin sharuddan samun beli, amma dai haryanzu ba’a bada belin nasa ba.”

Majiyar ta cigaba da bayani “dukkanin wadanda keda hannu cikin badakalar zasu shiga hannu, sai dai ni matsalata da shi shine, koda ma yana da sha’awar tsayawa takara, amma ya baya taimaka ma makwabtansa, saboda tun bayan bankado kudaden nan, jama’a da dama basu yi masa shedan kirki ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel