An bankado masana'antar jarirai a Arewa

An bankado masana'antar jarirai a Arewa

- Hukumomin tsaro a jihar Filato da ke Nijeriya, sun ce, sun kama wasu wasu mutane da suka hada maza da mata,da ake zargi da safarar jarirai

- An dai kama mutanen ne a Jos, babban birnin jihar, cikinsu har da wata mai ciki da ke gab da haihuwa

An bankado masana'antar jarirai a Arewa

An bankado masana'antar jarirai a Arewa

Hukumomi sun ce mutanen da aka kama dai sun hada da 'yan mata da akan yi wa ciki su haihu domin sayar da jariran da kuma wasu maza da ake zargi da ajiye 'yan matan suna yi musu ciki.

Manjo Janar Nicolas Rogers, shi ne kwamandan Rundunar Tsaro ta Musamman da ke aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato.

KU KARANTA: Wani katon banza ya kashe mahaifiyar sa

Ga kuma karin bayanin da ya yi kan kamun da suka yi, a hirarsa da Ishaq Khalid.

A wani labarin kuma, Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta kama wani mutum da kwanso saba'in da uku na hodar ibilis, yayin da yake yunkurin fita daga Nijeriya zuwa Dubai, dake Hadaddiyar Daular Larabawa.

An kama mutumin mai shekara 49 ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja babban birnin Nijeriya yayin binciken matafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel