Karanta labarin malamin da ya ki magana tsawon shekara 25

Karanta labarin malamin da ya ki magana tsawon shekara 25

-Wani sanannen malamin addinin muslunci mai suna Shehi Bashir Muhammad Bashir ya rufe bakinsa gum ya kuma ki magana tun cikin shekarar 1990

-Duk tambayar da aka yi masa da rubutu ya ke bayar da amsa, ya kuma ce ba zai yi magana ba sai lokacin da Allah Ya nufe shi

Sheikh Bashir Malamin da ya ki magana tsawon shekara 25
Karanta labarin malamin da ya ki magana tsawon shekara 25

A cewar wani rahoto, sheihun malamin dan kasar Sudan na magana da mutane ne kadai ta hanyar rubutu a kan takarda, amma ba da baki ba.

Kuma hakan ya ke yi a duk lokacin da ya bayyana a shirye-shiryen talbijin da aka yi a kan sa da kuma irin wannan baiwa da Allah ya ba shi ta kin magana.

An haifi Shehun Malami Bashir a shekarar 1956, ya kuma halarci fitacciyar jam'iar nan ta Sorbonne ta kasaa Faransa, a inda ya samu Digiri a kan kimiyyar tattalin arziki kafin ya dawo Sudan, a cewar rahoton.

Bayan ya dawo ne sai ya mayar da hankalinsa kan bincike da karatun Al'kur'ani maigirma, ya kuma yanke shawarar daina magana da kowa, sannan ya kuma ce ba zai yi magana ba sai lokacin da Allah ya nufe shi.

A hirar da aka yi da shi, yana rubuta amsoshinr tambayoyin da ake yi masa, malamin ya ce, sirrin wannan kame baki da daina magana da kowa, wani sirrinsa ne tsakaninsa da Ubangijin da ya halicce shi.

A shirin Talbijin din ya ce, a cikin rubutu, ba ya nadamar matakin da ya dauka na rashin magana, sannan ya kuma rubuta; "alkalamina na rubuta abin da ya ke faranta ran wadanda na ke tare da ni ne kawai. domin ni dai na amu kwanciya hankali a kame bakina" .

Allah daya gari ban-ban

Ga hoton bidiyon ra'ayi jama'a kan rashin lafiyar shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel