Za’a rantsar da shugaban kasar Gambia Adama Barrow

Za’a rantsar da shugaban kasar Gambia Adama Barrow

Sabon shugaban Gambia, Adama Barrow zai sha rantsuwar kama aiki a karo na biyu a ranar Asabar bayan Yahya Jammeh wanda ya mulki kasar sama da tsawon shekara 20, ya fice a cikin watan jiya.

Za’a rantsar da shugaban kasar Gambia Adama Barrow

Bikin rantsuwar ya zo daidai lokacin da Gambia ke cika shekara 52 da samun 'yancin kai.

Ana sa ran dubban mutane ciki har da shugabannin Afirka da dama za su halarci bikin rantsuwar a babban filin wasan ƙasar da ke Banjul.

KU KARANTA KUMA: Sakon ranar haihuwa mai taba zuciya da Zahra Buhari ta aika ma Aisha Buhari

An rantsar da shugaba Barrow a wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a cikin Senegal mai makwabtaka, kafin mutumin da ya kayar, Yahya Jammeh ya sauka daga mulki.

Sai da manyan kasashen Afirka ta yamma suka tura sojoji don tabbatar da ganin Jammeh ya bar mulki bayan tun da farko ya sauya magana a kan sakamakon zaben watan Disamba.

Tuni dai aka saki fursunonin siyasa da dama yayin da ƙasar ke shirin sake shiga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da kuma ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel