Tabarbarewar kasa: Wani mawaki yace babu laifin Buhari

Tabarbarewar kasa: Wani mawaki yace babu laifin Buhari

– Wani fittacen Mawaki yace duk babu laifin Buhari a matsalar da kasa ke ciki

– Charley Boy yace shugabannin baya su ka kashe Najeriya

– Ana dai fama da matsaloli da dama a Najeriya

Tabarbarewar kasa: Wani mawaki yace babu laifin Buhari
Tabarbarewar kasa: Wani mawaki yace babu laifin Buhari

Ana fama da matsaloli iri-iri a kasar nan sai dai wani fitaccen Mawaki a kasar yace duk babu laifin shugaba Buhari a duk abubuwan da ke faruwa. Mawakin Charley boy yayi kaurin suna wajen harkar tseren babur a Birnin Abuja

Mawakin yace duk laifin matasa ne da suka yi sake aka rika kwallo da su kamar kwallon giginya. Charley Boy yace matasa masu tasowa sun tsaya ne suna jiran lokacin su kurum yayi su ma su shiga wawurar kudin al’umma.

KU KARANTA: Trump ya soki Tsohon shugaba Barack Obama

Charley Boy ya kira mutanen kasar nan da su guji ruduwa da sunan kabila ko addini. Kwanaki dai ya rubuta wata budaddiyar wasika ga Inyamuran kasar masu neman Biyafara inda ya kira su da su farga. Charley Boy yace an dade da kashe kasar nan tun ba yau ba, Mawakin yace babu laifin Buhari inda ya hada da yi masa addu’a.

A yau Majalisar kula da tattalin arziki na kasa watau NEC ta zauna ta kuma nemi Gwamnan babban bankin CBN yayi wani abu game da yadda Naira ta fadi war-was. Yanzu haka dai Dalar Amurka tana kan N516 a kasuwar canji wanda tana iya kai N1000 inji wani masanin tattali.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Online view pixel