Gwamnatin tarayya zata miƙa Zakzaky hannun gwamnatin jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya zata miƙa Zakzaky hannun gwamnatin jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin mika shugaban kungiya’a yan shi’a El-Zakzaky ga hannun gwamnatin jihar Kaduna don gurfanar da shi gaban kotu.

Gwamnatin tarayya zata miƙa Zakzaky hannun gwamnatin jihar Kaduna

Hakan ya biyo bayan wata yarjejeniya da gwamnatin jihar ta shiga tsakaninta da gwamnatin tarayya wanda a yanzu haka ministan shari’a Abubakar Malami ya rattafa hannun kan wasu takardu dake nuni ga hakan.

Majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewar gwamnatin jihar Kaduna ce da kanta ta bukaci a miko mata Zakzaky don ta gurfanar da shi gaban kotu, kuma ta dade tana bibiyin bukatar tata, amma sai wannan karon ne gwamnatin tarayya ta amince.

KU KARANTA: Gwamnati ta kammala tsatstsaran tsarin farfado da tattalin arzikin kasa

Gwamnatin jihar ta bukaci a bata El-Zakzaky ne don gabatar da shi gaban kotu kan laifukan da tace ya aikata a jihar tun sama da shekaru 30 da suka gabata, amma dai har zuwa lokacin da muke hada wannan rahoton, ba’a rigaya an mika malamin hannun gwamnatin jihar ba, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Sai dai wasu na ganin wannan karon tsaye ne ga hukuncin babbar kotun tarayya dake Abuja wanda tace a saki malamin, kuma a gina masa sabon gida a duk jihar Arewa wanda yake so, tare da biyansa diyyar tauye masa hakkin dan adam dinsa.

A satin daya gaba ne kungiyar shi’a ta koka kan yadda lafiyar malamin nasu ke cigaba da tabarbarewa, inda ta bukaci a sakar mata shi, don bashi isashshen kulawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel