Masarautar Daura ta sauke Qur’ani sau 11 kan lafiyar Buhari

Masarautar Daura ta sauke Qur’ani sau 11 kan lafiyar Buhari

- Masarautar Daura ta gudanar da addu’a kan lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk ne ya jagoranci addu’an

- Abubuwan da aka shirya na addu’an ya hada da saukan al’Qur’ani mai girma sau goma sha daya

Masarautar Daura ta sauke Qur’ani sau 11 kan lafiyar Buhari

A ranar Juma’a, 17 ga watan Fabrairu, mazauna garin Daura sun gudanar da addu’a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Nation ta ruwaito cewa kungiyar karkashin jagorancin sarkin Daura Alhaji Umar Farouk sunyi addu’a sosai, don neman kariyan Allah da kuma samun lafiya ga shugaban kasa Buhari.

An bayyana cewa dubban jama’a mazauna Daura sun halarci addu’an.

KU KARANTA KUMA: Sakon ranar haihuwa mai taba zuciya da Zahra Buhari ta aika ma Aisha Buhari

A yanzu haka, shugaban kasa Buhari dan asalin garin Daura na hutu a birnin Landan inda yake kula da lafiyarsa.

A halin yanzu, da yake jagorantar addu’an, Farouk yace shugaban kasar na bukatar addu’a ba wai don lafiyarsa kawai ba amma harda kariya gurin gudanar da al’amuran kasar.

“Shugaban kasa danmu ne kuma ya cancanci fiye da haka," cewar Farouk.

Ya kuma tabbatar wa jama’ar Daura cewa babu wani matsala game da lafiyar shugaban kasa.

Sarkin yace yana matukar muhimmanci sanin cewa shugabanni na bukatar yawan addu’a daga al’ummansu.

Har ila yau, Shugaban limamai na manyan masallatan juma’a dake Daura, kanannan hukumomin Mai’adua, Zango, Sandamu da kuma Baure karkashin masarautan sun gudanar da addu’oi.

Addu’oin sun hada da saukar al’Qur’ani mai girma sau goma sha daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel