Yadda muka yi da IBB-Inji Atiku

Yadda muka yi da IBB-Inji Atiku

– Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai ziyara gidan tsohon shugan kasa IBB

– Atiku Abubakar yace ba zai fadi abin da su ka tattauna da Babangida ba

– Turakin Adamawa yace yanzu an sha shi yayi hankali

Yadda muka yi da IBB-Inji Atiku
Yadda muka yi da IBB-Inji Atiku

Kwanan nan ne Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyara gidan tsohon shugan kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidan sa da ke Minna. Sai dai ba a san ko me manyan kasar suka tattauna ba.

Atiku Abubakar yace yanzu an sha shi yayi hankali don haka ba zai bayyana irin wainar da suka toya tare da IBB din ba. Atiku dai ya gana da Babangida na fiye da awa biyu a gidan na sa. Turakin Adamawa yace ba zai bayyana ganawar ta su ga Duniya ba.

KU KARANTA:

Alhaji Atiku Abubakar yace idan har zai ba Gwamnati shawara ba a gidan jarida zai yi magana ba. Atiku Abubakar yace ba karamin cin mutunci bane ya fito yayi irin wannna magana a gaban duniya. Kwanan nan dai Janar Babangida ya dawo daga kasar waje daga ‘yar rashin lafiya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi tazarce watau zai yi shekara 8 a kan mulki inji Sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Babachir David Lawal. Babachir yace shugaba Buhari zai ba marada kunya, wanda wasu dai har fata suke yi ya mutu. Babachir din yace da yardar Ubangiji.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel