Shin addinin musulunci yana hura wutar ta'ddanci?

Shin addinin musulunci yana hura wutar ta'ddanci?

- A lokuta da dama musulmai na shan wahala wajen kokarin kare addinin musulunci musamman ma wajen wadan da ba musulmai ba

- Yawancin mutane sukan dauka addinin musulunci yana taimakawa wajen hura wutar ta'addanci ko kuma yana tauye hakkin mata da dai sauran su

A lokuta da dama ma dai da wuya musulmi ya shafe wani tsawon lokaci ba tare da an sa shi dole ya kare kansa ko addinin sa ba daga wata mummunar fahimta da akayi ma sa.

Wannan kuma yana zuwa wani lokaci ne saboda wasu hallayar musulmai da dama daga cikin mu da dabi'un su basu da kyau kwata-kwata wanda hakan yakan sa wadan da ba musulmai ba su dauka yin hakan musulunci ne.

To a yanzu dai abun ya kara kazanta musamman ma dai da hankalin duniya ya karkata wajen yaki da ta'addanci wanda kuma mafi yawan wadan da ake yaka da muguwar akidar suna kiran kansu musulmai na. Daga Iran zuwa Iraqi zuwa Somaliya har zuwa Najeriya ma.

So da yawa wadan da ke ikirarin yin hakan saboda addini sukan dauki wata aya ce a cikin alqu'ani su fassara ta baibai ko kuma susa san rai a cikin ta domin aiwatar da muguwar manufar su.

Ga dai abun da musulunci ya ce game da yaki da kuma fada nan a takaice:

"Allah ba yana hana ku ku aiwatar da hukunci ko ramuwa ga wadanda suka zalunce ku ba. Tabbas Allah yana son masu kyautatawa." (60:8)

Haka ma sadda manzon tsira Annabi Muhammad ya aike da sahabansa a fagen daga ce masu yayi:

"Kuje ku kare addinin Allah amma kada ku kashe tsofaffi, da yara da mata. Ku kuma yada kyakkyawan aiki domin Allah yana son kyautatawa" (Abu Dawud)

Haka ma dai wannan tafarkin shine Sayyidina Abubakar ya tabbatar lokacin mulkin sa inda shima ya umurci musulmai mayakan sa da kada su kashe mata da kananan yara da Tsaffi da gajiyayyu da ma itace. Ya kuma ce kada a kona wuraren ibada kada kuma a kashe dabbobi.

Tabbas addinin musulunci ya ba musulmai dama su tashi su kare kansu da kansu da kuma dukiyar su idan har abokan gaba sun far musu amma an saka adalci a cikin yadda hakan zata faru.

Hakan na kunshe cikin wata ayar Qur'ani kamar haka:

"Ya ku wadanda kuka yi imani ku tsaya tsayin daka ga Allah sannan kuma kuyi adalci cikin dukkan al'amuran ku. Kuyi adalci don shine kololuwar imani sannan kuma kuji tsoron Allah. (5:8)

Kuma Qur'ani mai girma ya bayyana karara cewa kashe rai babban laifi ne a cikin wannan ayar:

"Mun hukunta cewa dukkan wanda ya kashe rai ba ta hanyar shari'a ba to kamar ya kashe dukkan al'umma ne haka wanda ya kubutar da rai tamkar ya kubutar da dukkan al'umma." (5:32)

Asali: Legit.ng

Online view pixel