ALBISHIR: Gwamnatin tarayya ta amince tayi karin albashi

ALBISHIR: Gwamnatin tarayya ta amince tayi karin albashi

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya, Ayuba Wabba ya ce an cinmma matsaya tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar domin sake duba batun kara yawan mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata a kasar.

ALBISHIR: Gwamnatin tarayya ta amince tayi karin albashi
ALBISHIR: Gwamnatin tarayya ta amince tayi karin albashi

Wabbba ya bayyana haka ne yayin zantawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN a birnin Abuja.

Shugaban kwadagon ya ce nan bada dadewa ba za’a kafa kwamiti na musamman mai wakilai daga bangaren gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da kuma bangaren kungiyar kwadagon da zasu tantance tare da cimma matsaya kan yawan albashin mafi karanci.

KU KARANTA: Saura aiki kawai, mun tara N5triliyan - Osinbajo

A baya dai kungiyar kwadagon ta gabatarwa gwamnatin Najeriya bukatar kara yawan mafi karancin albashin ma’aikata a kasar zuwa naira dubu hamsin da shidda.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Najeriya ta bawa rundunar ‘yan sandan kasar, daukar sabbin jami’ai dubu goma a duk shekara, domin kawo karshen rashin yawan jami’an tsaron da kasar ke fuskanta.

Babban Sifeton ‘yan sandan kasar Ibrahim Idris ya tabbatar da samun cigaban, yayinda yake jagorantar wani taro da manyan jami’an ‘yan sanda a birnin Abuja.

Sifeto Janar Idris, ya ce Karin ya zama tilas domin samun nasarar murkushe aikata miyagun laifuka a kasar.

Ya ce kara yawan jami’an ‘yan sandan zai canza alkalumman da ke aiki a Najeriya, da ya nuna cewa dan sanda guda ne ke lura da mutane 400 a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel