Haka ubangiji ya kaddara in dinga sata – Barawon mota

Haka ubangiji ya kaddara in dinga sata – Barawon mota

An damke wasu barayin mota a karamar hukumar Saki na jihar Oyo kwanakin nan, kuma daya daga cikinsu yace haka ubangiji ya kaddara masa ya dinga sata.

Haka ubangiji ya kaddara in dinga sata – Barawon mota
Haka ubangiji ya kaddara in dinga sata – Barawon mota

Game da cewar jaridar The Nation, wani jibgegen barawo da aka damke a Saki yace fa shi ba yin kansa bane satan da yakeyi, innama kaddarar da mahallincinsa yayi masa ne.

Barawon mai suna Hussein Mohammed, ya fada ma jamián yan sanda da yan jarida cewa kaddaransa kenan ya dinga sata saboda ai ubangiji ya hallici alheri da sharri, kuma shi ya taba zama a kurkuku saboda irin wannan laifi.

KU KARANTA: White House ta tabbatar da wayan Trump ga Buhari

Fitowanshi daga kurkuku ke da wuya, sai ya kara halin beran tare da wasu abokansa Salawu Nurudeen, Oriowo Ayo, Ahmadu Garuba da Ogunbiyi Kola.

Game da cewar kwamishanan yan sandan jihar Legas, Mr. Sam Adegbuyi, an damke su ne a watan Nuwamba akan laifin sata.

Yayinda aka tattauna da wani wanda sukayi wa sata, Alhaji Badmus, yace :

“Yan fashin sun shiga gidana a Saki ranan 21 ga watan Nuwamba,2016 misalin karfe 7:45 na dare kuma suka tsare iyali na. yayinda na dawo misalin karfe 9:50 a dare, na kira iyali na a wata da diya ta, ashe yan fashin na rike da su.

Ina shigowa gida, 2 daga cikinsu suka fito suna daura mini bindiga a kirji. Da na fara kallon su, daya daga cikinsu yace ‘cigaba da kallonmu; dama an ce mana kanada taurin kai,’sun yi mini gargadi saboda iyali na da ke cikin gida.

Sai na mika wuya har muka shiga gidan, daya daga cikinsu ya haska mini mari. Sun bukaci gwala gwalai, kudi, risidin talabijin di na da agogon da na sayo daga Makkah lokacin da na je hajji."

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Asali: Legit.ng

Online view pixel