Farashin danyen mai a kasuwan duniya ya sake sauka zuwa $56.25

Farashin danyen mai a kasuwan duniya ya sake sauka zuwa $56.25

Farashin man fetur ya sauka a jiya bisa ga kokarin kasar Amurka wajen samar da man fetur da kuma hassadan wasu kusoshi akan yunkurin da kungiyar kasashe masu fitar da mai wato OPEC sukayi na rage fitar da mai har sai kudin ya tashi.

Farashin danyen mai a kasuwan duniya ya sake sauka zuwa $56.25
Farashin danyen mai a kasuwan duniya ya sake sauka zuwa $56.25

A yau, danyen man fetur ya sauka zuwa $56.25 amma na kasar Amurka na West Texas na $53.45.

Masu hakan man kasar Amurka sun zangen damtsen hakan mai sosai a wata da ya gabata wanda ya sa sunada rijioyin mai 591 game da cewar Baker Hughes.

KU KARANTA: Boko Haram ta kashe wani malamin addini

Dalilin wannan abu shine kasar Amurka na yaki da shawaran kungiyar kasashe masu fitar da mai wato OPEC na rage fitar da man fetur domin kudin man a kasuwan duniya ya kara daraja. Kasashen OPEC wanda hada da kasar Rasha sun amince a 2016 cewa za’a rage fitar da randar danyen mai 1.8 millon a kowani rana na tsawon wata 6 a wannan shekarar.

An sa ran kungiyar zata fitar da rahoton ta na farko kan wadanda suka bi shawaran, jiya. An samu cewa kasha 92 sun bi wannan umurni.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Asali: Legit.ng

Online view pixel