Boko Haram sun kashe wani Malamin Addini

Boko Haram sun kashe wani Malamin Addini

– Kungiyar Boko Haram sun kai hari a wani Gari da ke kusa da Chibok

– ‘Yan ta’addan sun kashe wani Malamin addini

– Tuni dai Sojoji su ka yi abin da ya dace

Boko Haram sun kashe wani Malamin Addini
Boko Haram sun kashe wani Malamin Addini

Yayin da wasu ‘Yan Boko Haram ke kokarin tserewa sun kai hari a wani Gari da ke kusa da Chibok mai suba Mifa a Jihar Borno. Sanadiyar haka dai an kashe wani Malamin addini sannan kuma an karyawa wani yaro hannu.

‘Yan Boko Haram din dai suna neman wurin guduwa ne don kuwa sun ta harbin iska. Ko da ‘Yan Garin suka ga halin da ake ciki sai suka nemi agajin Sojojin da ke can cikin Garin Chibok. Kafin kace mene kuwa Sojin suka kawo doki.

KU KARANTA: Amurka za ta taimakwa Najeriya

Sojojin Najeriya dai sun kashe wani daga cikin ‘Yan ta’addan wanda sun haura mutum 30. Matsalar dai Garin Chibok na zagaye ne da daji, yanzu haka kuma an fatattako ‘Yan Boko Haram daga Dajin Sambisa.

Shekaran jiya shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayi magana da shugaban kasar Amurka Donald Trump a waya daga gidan sa a Landan. Trump din ya jinjinawa Buhari wajen yaki da Boko Haram ya kuma yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen karasa murkashe ‘yan ta’addan.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Soja ga wuta ga yaki

.

Asali: Legit.ng

Online view pixel