'Za'a sauya fasalin ƙasar nan matuƙar ýan Najeriya sun so' - Atiku

'Za'a sauya fasalin ƙasar nan matuƙar ýan Najeriya sun so' - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar yace batun mika mulkin kasar nan ga yankin Inyamurai yana hannun al’ummar Najeriya ne.

'Za'a sauya fasalin ƙasar nan matuƙar ýan Najeriya sun so' - Atiku

Atiku ya bayyana haka ne yayin dayake amsa tambayoyi daga yan jaridu bayan wata ganawar sirri da yayi da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida a gidan sa dake garin Minna jiya Talata 14 ga watan Feburairu, inda yace yanke irin wannan shawara na bukatar goyon yan Najeriya.

“Zancen sake fasalin kasar nan ba aikin mutum daya bane ya yanke yadda za’ayi, a’a. yan Najeriya ne kawai zasu iya tantance yadda za’ayi game da canza fasalin Najeriya.”

KU KARANTA: ‘Ya dace shugaba Buhari yayi ma yan Najeriya jawabi ko dan yaya’ – inji Farfesa Akin

Dayake bayani kan dalilin zuwansa, Atiku yace “na zo ne musamman don kawo ma janar Babangida ziyara, tare da yi masa fatan Alheri.”

Da aka tambaye shi game da wace shawara zai baiwa gwamnatin tarayya game da halin da kasar ke ciki a yanzu, Atiku yace ba a shafukan jaridu ya kamata ya baiwa gwamnati shawara ba.

“Idan ina da wata shawara da zan baiwa gwamnati, toh zan tunkare su ne gaba da gaba, ba wai a shafukan jaridu ba.” Inji shi.

Jigon jam’iyyar APC ya samu rakiyar Kyeftin Yahaya Gombe, Ambasada Yahaya Kwande, Alhaji Kwaronga Jada da Alhaji Jamilu Jibrin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel