Barcelona ta ji kunya a hannun PSG

Barcelona ta ji kunya a hannun PSG

– PSG ta yi kaca-kaca da Barcelona a Gasar Champions League

– An durawa Barcelona har ci 4 ba ta ce komai ba

– Di Maria ya jefa kwallaye biyu

Barcelona ta ji kunya a hannun PSG
Barcelona ta ji kunya a hannun PSG

Kungiyar Barcelona ta sha dan banzan kashi hannun Kungiyar PSG ta Faransa a Gasar UEFA Champions League. Kungiyar PSG din dai tayi wa Barcelona kaca-kaca ne a filin wasan ta da ke Garin Paris.

Dan wasa Angel Di Maria ne dai ya koyawa su Lionel Messi da Suarez hankali. Di Maria ya zuba wata firinkit kafin minti 20 da take wasa ya kuma kara wata a Minti na 55. Har aka tashi rabin lokaci dai Barcelona ba tayi wani abin kirki ba.

KU KARANTA: Ana cigiyar wata budurwa a Kano

Barcelona ta ji kunya a hannun PSG
Barcelona ta ji kunya a hannun PSG

Sabon dan wasa Draxler ya jefa kwallo guda bayan dan wasan Barcelona Lionel Messi yayi sakaci. Daga karshe dai Edison Cavani ya jefa kwallo guda a ragar Barcelona bayan ya zubar da wani kwallon a baya.

Da kyar dai idan ba Barcelona ta fita daga Gasar a zagaye na rubu’in karshe ba. Kafin dai Barcelona ta fito sai ta zubawa PSG kwallaye akalla biyar da nema a Kasar Spain idan an sake haduwa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel