Gurgun da sojoji suka casa ya samu gwaggwaɓan kyauta daga gwamnan Ebonyi

Gurgun da sojoji suka casa ya samu gwaggwaɓan kyauta daga gwamnan Ebonyi

Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya baiwa gurgun nan, Chijoke Oratu kyautan N500,000 wanda sojoji suka tumurmusa a garin Onitsha don ya sanya Khakin soji.

Gurgun da sojoji suka casa ya samu gwaggwaɓan kyauta daga gwamnan Ebonyi
Gurgun da sojoji suka casa ya samu gwaggwaɓan kyauta daga gwamnan Ebonyi

A yayin da Umahi ke tarbar gurgu Chijoke wanda dan asalin jihar Ebonyi ne, a fadar gwamnatin jihar ya bukaci hukumar soji ta sallami sojojin daga bakin aiki tare da gurfanar dasu gaban kotu sakamakon cin zarafin Chijoke da suka yi.

Nan take gwamnan ya baiwa gurgun kyautan naira dubu dari biyar a matsayin tallafi, sa’annan yayi alkawarin tallafa mai da jari don fara kasuwanci.

KU KARANTA: ‘Atiku zai yi takarar shugaban kasa a PDP a 2019’ – inji jigon PDP

Gurgun da sojoji suka casa ya samu gwaggwaɓan kyauta daga gwamnan Ebonyi
Gurgun da sojoji suka casa a fadar gwamnantin jihar Ebonyi

A satin daya gabata ne bidiyon tumurmusan da sojoji suka yi ma Chijoke ya watsu a yanar gizo, inda aka hangi sojojin suna wancakalar da gurgun daga kan kekensa yayin da jama’a ke ta kallo sun kasa yi masu komai, wanda hakan ya janyo fushin al’umma, kuma ya sanya hukumar sojin kama sojojin su biyu.

Kaakakin rundunar soji Birgediya Sani Usman ya sanar da kama sojojin da suka aikata wannan danyen aiki, Bature Samuel da Abdulazeez Usman, masu matsayin kofur, inda yace a yanzu haka an hukuntasu ta hanyar rage musu girma tare da dauresu na tsawon kwanaki 21 da horo mai tsanani.

Daga karshe gwamnan ya umarci mashawarcinsa akan tallafa ma mutane daya tattauna da iyalan Chijoke don nemo hanyar sake tsugunar da shi.

Ga bidiyon dukan nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel