Wani Dan wasan Najeriya ya mutu ana tsakiyar wasa

Wani Dan wasan Najeriya ya mutu ana tsakiyar wasa

– Wani Dan wasan Najeriya ya fadi ya mutu a filin kwallo

– Dan wasa Henry Obiekwu ya mutu ana tsakiyar wasa

– Marigayin ya kasance yana bugawa Kungiyar Enugu Rangers

Wani Dan wasan Najeriya ya mutu ana tsakiyar wasa
Wani Dan wasan Najeriya ya mutu ana tsakiyar wasa

Kwallon kafan Najeriya dai ta gamu da abin takaici bayan da wani Dan wasan Kungiyar Enugu Rangers na gida ya fadi matacce ana tsakiyar wasa jiya Litinin 13 ga wannan wata .

Tauraron Dan wasan Henry Obiekwu ya kwanta dama ne a jiya bayan ya buga wani wasa na kawance tsakanin Kungiyar ta su da ta Samba FC. Dan wasan yayi kukan ciwon kirji hakan ta sa aka cire sa daga wasan.

KU KARANTA: Farashin mai zai tashi a Najeriya

Dan uwan dan wasan wanda ya kuma taba bugawa Super Eagles Kingsley Obiekwu ya tabbatar wa Africanfootball cewa dan uwan na sa Henry ya rasu. An dai yi kokarin wucewa da dan wasan Asibitin Eastern Nigeria Medical Centre a Birnin Enugu inda a can ya ce ga garin ku.

A Ingila kuma wasu tsageru sun kai hari gidan wani dan wasan Liverpool saboda jin haushin ya zubar da finariti a Gasar cin kofin nahiyar Afrika. Dan wasa Mane ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida Gasar AFCON, wasu suka ce da gan-gan yayi hakan.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel