Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta ma ýaýa-mata yin talla

Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta ma ýaýa-mata yin talla

Gwamnatin jihar Jigawa a karkashin kagorancin gwamna Abdullahi Badaru ta kammala shirin fara tabbatar da dokar hana kananan yara mata tallace tallace akan titi, sakamakon yawan fyade a jihar.

Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta ma ýaýa-mata yin talla
Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta ma ýaýa-mata yin talla

Kwamandan hukumar Hisbah na jihar, Aminu Baba Waziri ne ya bayyana haka a jiya Lahadi 12 ga watan Feburairu yayin dayake yi ma manema labaru karin bayani a garin Dutse.

KU KARANTA: Abin al'ajabi: ƙaramar yarinya ýar shekara 5 ta haihu

Kwamandan yace zasu cigaba da wayar ma jama’a kai dangane da illolin talla ga yan mata kanana, kafin su fara tabbatar da bin dokar. Ya kara da cewa ya zama dole su wayar ma jama’a kai, sakamakon yadda wasu iyaye ke fakewa da sunan talauci, suna sanya rayuwar yayansu cikin hatsari da tallace tallace.

Kwamandan ya koka kan yadda ake cutar da yaya mata, inda yake cewa “idan kaje unguwannin Yalwawa da Yan tifa, a cikin garin Dutse, zaka ga yadda yan mata ke kaiwa har tsakar dare suna yawo da sunan talla.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel