Matasan Musulmai sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da ranar masoya

Matasan Musulmai sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da ranar masoya

Dalibai musulmai sun gudanar da zanga zangar a ranar Litinin 13 ga watan Feburairu a can kasar Indonesia na nuna rashin kiyayyarsu da bikin ranar masoya da ake yi duk a shekara 14 ga watan Feburairu, wato rana mai kamar ta yau.

Matasan Musulmai sun gudanar da zanzangar kin amincewa da ranar masoya
Matasan Musulmai sun gudanar da zanzangar kin amincewa da ranar masoya

Daliban sun bayyana ranar a matsayin wata ran ace da turawan yamma suka ware don karfafa ma matasa gwiwar yin zinace zinace.

Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa mafi yawan matasan da suka gudanar da zanga zangar yan shekaru 13 ne zuwa 15, ciki har da yan mata sanye da dan kwalaye suna kiran ‘ba ruwan mu da ranar masoya’ wato Valentine.

Wanda ya shirya zanga zangar, Pandu Satria yace “mun shirya wannnan gangami ne don barranta kanmu daga bikin Valentine, wanda muka gano shiri na turawa don halasta zina.”

KU KARANTA: Uwar bari?: ‘A shirye nake nayi sulhu da Kwankwaso’ – Ganduje

Wannan dai shine ganganmin nuna kiyayya ga ranar masoya na kwana kwanan nan da aka yi a kasar ta Indonesia, a yayin da wasu matasan kuma ke amfani da ranar da sunan bayyana ma junansu kauna da soyayya.

Matasan Musulmai sun gudanar da zanzangar kin amincewa da ranar masoya
Matasan Musulmai sun gudanar da zanzangar kin amincewa da ranar masoya

Shima shugaban makarantar, Ida Indahwati Maliulu yace “abin alfahari ne a gare ni yadda dalibai na suka yi tir da bikin ranar masoya.”

Haka zalika an haramta bikin ranar masoyan a birane da daman a kasar Indonesia. Suma a kasar Malaysia, inda addinin musulunci ne mafi rinjaye, an samu wata kungiya mai suna kungiyar matasa muslmai ta kasa wanda tayi kira ga yan mata da su guji amfani da turare mai kamshi kafin zuwan ranar Valentine.

Kungiyar tace mutane ka iya amfani da ranar masoyan don nuna kin amincewarsu da ita ta hanyar buga takardun kin amincewa da kuma kin sanya irin kayan da ake amfani dasu a ranar.

Sai dai jama’a da dama a kasashen Indonesia da Malaysia suna gudanar da bikin Valentine din, musamman a manyan biranensu, inda zaka ga mutane na raba alawa da katunan gaisuwa irin na soyayya.

Ko a shekarar 2015, majalisar malamai musulmai ta kasar Indonesia sun yi barazanar fitar da fatawa na hana siyar da kwaroron roba, biyo bayan rahotanni da suka bayyana inda ake cewa wai ana siyar da kwaroron robar ne tare da alewa don bikin zagayowar ranar masoya ta Valentine.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel