LABARI DA DUMI-DUMI: Tsohon gwamnan jihar Taraba na fuskantar barazanar zuwa gidan yari

LABARI DA DUMI-DUMI: Tsohon gwamnan jihar Taraba na fuskantar barazanar zuwa gidan yari

- Tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame na fuskantar barazanar dauri a gidan yari

- Hukumar tattalin arziki da Laifukan kudi EFCC na zargin tsohon gwamnan da almubazzaranci da kudin jihar a lokacin da ya ke gwamna

LABARI DA DUMI-DUMI: Tsohon gwamnan jihar Taraba na fuskantar barazanar zuwa gidan yari
Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame

Tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame ya rasa dakatar da hukumar tattalin arziki da Laifukan kudi (EFCC) na gudanar da shi a kotu.

Nyame, wanda hukumar tattalin arziki da Laifukan kudi EFCC ya gabatar a kan zargin laifi handama da kuma almubazzaranci da wasu kudadin jihar kimani biliyan N1.6 wadda ya ke neman babban kotun kasa ta dakatar da EFCC na gudanar da shi, amma Justice Adebukola Banjoko ta yi watsi da harkan a ranar Talata, 14 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Kiristocin jihar Borno sun fara azumi na kwana 7 saboda shugaba Buhari

Jaridar Punch ta rawaito cewa Alkali Banjoko ta amince a gudanar da Nyame da ya amsa tambayar zargin almubazzaranci da kudi biliyan N1.6 da hukumar cin hanci da rashawa ke masa.

Alkalin ta daga saman zuwa watan Maris 8, 2017 a inda a ke bukata Nyame ya kare kansa.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel