Buhari zai dawo garau Inji PDP

Buhari zai dawo garau Inji PDP

– Shugaban bangaren PDP Ali Modu Sheriff yace Najeriya ba za ta iya zama ba shugaba Buhari ba

– Ali Sheriff shugaban kasa Muhammadu Buhari na nan dawowa garau

– PDP tace idan babu Buhari yaki da cin hanci da rashawa zai yi wahala

Buhari zai dawo garau Inji PDP
Buhari zai dawo garau Inji PDP

Shugaban wani bangaren PDP Alhaji Ali Modu Sheriff yace Najeriya ba za ta iya zama babu shugaba Muhammadu Buhari ba. Ali Sheriff yace idan har babu Buhari to yaki da cin hanci da rashawa ba zai yiwu ba.

Ali Modu Sheriff yace shugaba Buhari na nan dawowa garau cikin koshin lafiya. Kamar yadda muka samu labari daga Jaridar Daily Post. Jam’iyyar tayi wannan jawabi ne a wani taro da aka yi a Jihar Ogun, PDP tace Najeriya na bukatar Buhari.

KU KARANTA: Gwamna Shettima ya caccaki Ali Modu Sheriff

Shugaban bangaren na PDP Ali Sheriff yace zai cigaba da kokari wajen ganin Jam’iyyar ta dawo da karfin ta. Ana dai ta rikici a cikin Jam’iyyar tsakanin bangaren Ahmed Makarfi da kuma na Ali Sheriff.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayi magana da shugaban kasar Amurka Donald Trump ta waya daga gidan sa a Landan a jiya. Trump din ya jinjinawa Buhari wajen yaki da Boko Haram ya kuma yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen karasa murkashe ‘yan ta’addan.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel