Muhimman labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Muhimman labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Kamar yau da kullun, jaridar Legit.ng tanan kawo muku Takaitattun labaran abubuwan da suka faru jiya Litinin 13 ga watan Febrairu , a fadin Najeriya. Ku sha karatu

1. Akalla mutane 20 sun hallaka a rikici tsakanin jihar Akwa Ibom da Kross Riba

Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin
Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a wata rikicin kabila da ya faru tsakanin mutanen jihar Akwa Ibom da Kross Riba.

2. An samu magidanci a mace cikin dakin Otal a Aba

Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin
Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Jaridar Sun ta bada rahoton cewa mutumin mai suna, Peter Ibekwe, ya fadawa matarsa cewa zai tafi kasuwanci garin Umuahia kafin ya bar gida. Amma a maimakon tafiya, sai ya tafi dakin Otal da ke Club 25 road, Abayi Aba a karamar hukumar Osisioma.

3. Yau shekaru 41 kenan da kisan Janar Murtala Muhammad

Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin
Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

A rana irin ta yau a shekarar 1976 ranan 13 ga watan Febrairu ne aka kashe tsohon shugaban kasan soja, Janar Murtala Mohammed a wata yunkuri na juyin mulki da aka yi masa a ranan Juma’a 13 ga watan Febrairu.

4. Dan kwangila yayi gaba da N37m na kwalejin koyan tukin jirgi a Zariya

Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin
Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Wani dan kwangilan kwalejin koyan tukin jirgin sama NCAT da ke Zariya ya arce da kudi N37m wanda aka bashi na gina garejin jirgi.

5. Gwamna Shettima ya caccaki Ali Modu Sherrif akan Boko Haram

Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin
Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya soki magabacinsa Ali Modu Sherrif akan rashin kula wanda ya sabbaba yaduwan kungiyar Boko Haram.

6. Zamu taimaka muku da makamai; karanta sauran abinda Donald Trump ya fadawa Buhari

Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin
Muhimman laaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasar Amurka Donald Trump murna a kan nasararsa a zaben kasan Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel