Zamu taimaka muku da makamai; karanta sauran abinda Donald Trump ya fadawa Buhari

Zamu taimaka muku da makamai; karanta sauran abinda Donald Trump ya fadawa Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasar Amurka Donald Trump murna a kan nasararsa a zaben kasan Amurka.

Zamu taimaka muku da makamai; karanta sauran abinda Donald Trump ya fadawa Buhari
Zamu taimaka muku da makamai; karanta sauran abinda Donald Trump ya fadawa Buhari

Shugabannin kasan guda biyu sunyi Magana a ranan Litinin, 13 ga watan Febrairu bayan an sanar da cewa Buhari zai yi waya da shi mislamin karfe 3:45 na rana.

A wata jawabin da mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki, yace Trump ya jinjinawa shugaba Buhari game da nasarar da aka samu aka yakin Boko Haram kuma yayi alkawarin hadin kai da kasashen guda biyu.

KU KARANTA: Zakzaky ya far makancewa - Yan Shi'a

Kana kuma yace kasar Amurka zata taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci ta hanyar bamu makamai.

Karanta jawabin:

“Shugaba Muhammadu Buhari yayi Magana da shugaban kasa Donald Trump da ranan nan a waya bisa ga bukatar shugaban kasan Amurka.

Sunyi Magana mai dadi inda shugaba Buhari ya taya Trump murnan nasarar zaben sa a matsayin shugaban kasar Amurka.

Shugabannin biyu sun tattauna akan hanyoyin zurfafa hadaka wajen yaki da ta’addanci ta hanyar samar da makamai.

Shugaba Trump ya jinjinawa Buhari ya cigaba da aiki mai kyau da yakeyi, kuma yay aba masa akan kokarin ceto yan matan Chibok 24 da kuma kokarin da rundunar sojin Najeriya keyi.

Shugaba Trump ya tabbatar way an Najeriya cewa kasar Amurka na shirye da ta taimakawa Najeriya da makamai wajen yakan ta’addanci.

Kana kuma shugaba Trump ya gayyaci shugaba Buhari birnin Washington a lokacin da yake so.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

Asali: Legit.ng

Online view pixel