Hotuna: Yadda Buhari ke bin manufofin marigayi murtala bayan shekaru 41

Hotuna: Yadda Buhari ke bin manufofin marigayi murtala bayan shekaru 41

- Marigayi Murtala Mohammed ya gabatar da shugaba Muhammadu Buhari ga shugabanci

- Gwamnatin marigayin na tare da manufofin masu tsananin wanda shugaba Buhari ke koikoyo da har yanzu

Yadda Buhari ke bin manufofin marigayi murtala bayan shekaru 41

A wata bayyani da ya fito yadda marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed ya rinjayi manufar da tunanin shugaba Muhammadu Buhari wanda yake matsayin bayansa a soja a lokacin.

A lokacin da ya ba Najeriya hango akida, da mayar da hankali da kuma jagorancin mai adalci da al'umma ke bukata, wanda ya yi sanadiyar ‘yan Najeriya ke farin ciki da gwamnatin sa.

Yadda Buhari ke bin manufofin marigayi murtala bayan shekaru 41

Murnar ‘yan Najeriya na tare da samu shugaba mai adalci da kuma manufofin na cigaban al’umma gaba daya.

KU KARANTA KUMA: Yadda Obasanjo da Jonathan suka yaudari ‘yan Arewa – Inji Farfesa Ango

Wadannan halaye na marigayi Murtala ne Kanal Muhammadu Buhari a wannan lokaci wanda Murtala ya gabatar da shi ga shugabanci ya dauka har yanzu.

Ko da yake gwamnatin Murtala ba ta yi wata dadewa a mulki ba, kawai aka wayi gari a ranar Jumma'a, 13 ga watan Fabrairu, 1976 labari ya bazu cewa an kashe shugaban kasa Janar Murtala Ramat Muhammed a wata yunkurin juyin mulki a karkashin jagorancin Kanar Buka Suka Dimka.

Yadda Buhari ke bin manufofin marigayi murtala bayan shekaru 41

Tuni shugaba Murtala ya fara jawo hankali shugaba Buhari ga shugabanci bayan ya nada shi a matsayin gwamnan arewa maso gabas, wanda yanzu aka raba a matsayin jihohin 6, su ne Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.

KU KARANTA KUMA: Rashin dawowar Buhari, yan majalisar dokokin kasa zasu maida Osinbajo shugaban kasa?

Kafin nan akwai labarin yadda Murtala ya mika Lieutenant Buhari ga Gowon sabon shugaban kasa a lokacin a matsayin ADC mai wa shugaban kasa hidima.

Yadda Buhari ke bin manufofin marigayi murtala bayan shekaru 41

A lokacin da ya ke gwamna shugaba Buhari ya goyi bayan gwamnatin tarayya saboda ta yaki cin hanci da rashawa.

Bayan juyin mulkin watan Disamba 31, 1983, Buhari ya zama Shugaban kasa da mataimakinsa marigayi Manjo Janar Tunde Idiagbon, ya shaida wa 'yan Nijeriya cewa babu wata babbanci gwamnatin sa da na Murtala / Obasanjo, ya kuma yi alkawarin cewa za su gyara duk abin da suka samu ba dai-dai ba a arakokin gwamnati.

Yadda Buhari ke bin manufofin marigayi murtala bayan shekaru 41

Kuma a shekarar 1984, yayin da ya ke kokarin neman yadar ‘yan Nijeriya, Buhari ya ce: "Lalle ne, wannan zamani namu da kuma nan gaba ba wata kasa da zamu iya kira kasan mu da wuce Najeriya, dole ne mu kazance a nan saboda mu daukaka kasar mu tare."

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel