Kazamar zanga-zanga a wannan Kwalejin fasar (Karanta)

Kazamar zanga-zanga a wannan Kwalejin fasar (Karanta)

Daliban kolejin kimiyya da fasaha ta Ibadan sun yi zanga zangar ce domin nuna rashin yarda da kame shugabanninsu da 'yan sanda suka yi.

Kazamar zanga-zanga a wannan Kwalejin fasar (Karanta)
Kazamar zanga-zanga a wannan Kwalejin fasar (Karanta)

Daruruwan Daliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ibadan ne suka yi zangazanga domin nuna fushinsu sakamakon Kama shuwagaban nin su da Jami’an ‘Yan Sanda na jihar Oyo suka yi, Daliban na zargin rundunar Yan sandan ne da tsare Shuwagabannin nasu alokacin da suka je Belin wasu dalibai da aka kama a yankin Akwete.

KU KARANTA: Kun ji abun da Andrew Yakubu ya fada game da kudin da EFCC ta kwato hannun sa?

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Daliban yace Jami’an ‘Yan sanda sun je wani gida inda suka kama wasu dalibai a zaune a kofar gidan inda yan sandan suka zargesu da yin zanga zanga Sannan suka tsare shuwagabannin kungiyar da suka je belin su a Helikwatar Yan Sanda dake Ele-Ele, Shugaban ya bayyana cewa hakan bai dace ba kuma ya sabawa doka don haka a sako masu shuwagabannin su.

Mataimakin Jami’in Hulda da Jama’a na Polytechnic Ibadan Mr. Olayemi Boboyemi yace makarantar kimiyya Da Fasaha ta Ibadan ta sanya baki domin komi ya lafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel