Dan kwangila yayi gaba da N37m na kwalejin koyan tukin jirgi a Zariya

Dan kwangila yayi gaba da N37m na kwalejin koyan tukin jirgi a Zariya

Wani dan kwangilan kwalejin koyan tukin jirgin sama NCAT da ke Zariya ya arce da kudi N37m wanda aka bashi na gina garejin jirgi.

Dan kwangila yayi gaba da N37m na kwalejin koyan tukin jirgi a Zariya
Dan kwangila yayi gaba da N37m na kwalejin koyan tukin jirgi a Zariya

Kwamitin majalisar dattawan akan jirgin sama ta kai ziyarar bincike karkashin jagorancin mataimakin shugaban kwamitin ,Sanata Bala Na Allah a ranan Juma’a, inda yayi barazanar damde dan kwangilan da yayi gaba da kudin gina gareji da aka bashi.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa kwamitin ta je domin duba wasu ayyuka a a kwalejin kuma ta nuna bacin ranta akan garejin jirgin na 3 da ba’a karashe ba bayan an biya kamfanin Mushaj Fahaj Nigeria Ltd kudin ginawa.

KU KARANTA: An samu magidanci a boye a dakin Otal

Sanata Bala yayi barazanar cewa za’a damke dan kwangilan akan cewa an bashi kudi N37m kuma kasha 1 cikin 5 kawai yayi na aikin.

yayinda shugaban kwalejin, Captain Abdulsalami Mohammed, ke lissafa kalubalen da kkwalejin ke fuskanta, yace rashin kudin domin gudanar da ayyuka a kwalejn, tashin dalar Amurka akan ayyuka, rashin kudin canji, tsadan man jirgi, rashin isasshen malamai da kuma rashin isasshen ofis na ma’aikata ne manyan kalubalen da suke fuskanta.

Kana yace an gama wasu ayyuka wanda ya kunshi karashe filin jirgin koyo, wurin tsabtace ruwa, kayan aikin tsaro na filin jirgi da samun wasu manyan lasisin duniya.

Sauran mambobin kwamitin sune Sanata Ben Murray-Bruce, Mohammed Lafiagi, Rilwan Akanbi, Ahem Ogembe da Bala Na’ Allah.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel