Dan uwan Buhari, yayansa mata sun ziyarce shi a Landan

Dan uwan Buhari, yayansa mata sun ziyarce shi a Landan

- A yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari na hutu a gidan gwamnatin Najeriya dake birnin Landan

- Hukumar na yankin posh Campden Hill dake Borough of Kensington da Chelsea a Kudancin Landan

- Ana kiran gurin Abuja House (gidan Abuja) kuma ya kance daya daga cikin gidaje mafi girma a unguwar

Rahoto daga jaridar The Nation ta bayar da cikakken bayanin yadda gidan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke hutunsa yake tun lokacin da ya koma chan.

Shugaban kasar na ta tarban baki tun bayan da ya koma gidan wanda ke unguwar posh Campden Hill dake Borough of Kensington da Chelsea a Kudancin Landan.

Dan uwan Buhari, yayansa mata sun ziyarce shi a Landan

A ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu, shugaban kasa Buhari ya karbi bakoncin shugaban ma’aikata; Abba Kyari, gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun da kuma Sanata Daisy Danjuma.

Haka kuma Uwagidan shugaban kasar Aisha ta ziyarce shi sannan daga baya aka gansa tare da Gwamna Amosun suna cin abinci.

KU KARANTA KUMA: Ana shirin amfani da yan Boko Haram gurin kashe Nnamdi Kanu - IPOB

A makon da ya gabata, babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Cif Bisi Akande sun ziyarci shugaban kasa a gidan Abuja dake birnin Landan.

A cewar rahoton, dan uwan shugaban kasar, Alhaji Mamman Daura ya ziyarci shugaban kasa a jiya, 12 ga watan Fabrairu.

Rahoton ya kuma bayyana cewa da misalin karfe 1.05 na rana (agogon Landan), an fitar da wasu masu mata guda biyu da aka bayyana a matsayin ‘yayan shugaban kasa Buhari daga Abuja House cikin wani bakin mota kiran Mercedes Benz. Motar ya dawo da misalign karfe 2.24 na ran aba tare da pasinjojin ba.

Da karfe 1.20 na rana, Daura ya iso a cikin bakin motar aya na Landan. Ya kasance tare da wasu mutane biyu. Daura, wanda ya tafi da misalign karfe 2.50 na rana, yaki fadin komai da aka tambaye shi kan yadda shugaban kasa Buhari yake yace: “Na zo nan tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu rannan, baku gani bane?"

Jim kadan da misalin karfe 3.30 na rana, wasu jami’ai biyar – jami’an tsaro da aka dauko guda biyu da kuma wasu uku, wadanda suka kasance masu gadin gidan, da kuma wani mataimakin shugaban kasa na musamman, sun zo don tambayi mai kawo rahoto na gidan jaridan The Nation kan dalilin da yasa “yake yawo a gurin”.

KU KARANTA KUMA: ‘Buhari ba zai mutu ba, Allah zai kunyata masu yi mashi fatan mutuwa’

Anyi mai barazana sannan aka ce mai ya tafi don guje ma gayyatan yan sanda. “Ya zama dole ka bar nan da motar nan. Bazaka iya daukan ko wani hoto a nan ba,” cewar wani mai tsaro.

A halin yanzu, jam’iyyar APC sashin Landan ta shawarci yan Najeriya da su mayar da hankali ga tattalin arzikin Najeriya maimakon lafiyar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel