Yan kabilar Jonathan zasu yi gangamin kin jinin Fulani

Yan kabilar Jonathan zasu yi gangamin kin jinin Fulani

- Matakin da gwamnatin jiyar Bayelsa ta dauka na baiwa fulani makiyaya burtalin kiyo na ci gaba da tayar da kura a jihar bayan da wasu kungiyoyi da mata a jihar suka hau kujerar naki

- Jaridar Vanguard ta ruwaito cewar kungiyoyin sa kai da kuma mata a jihar suna shirin yin gangamin nuna rashin amincewar su da matakin da Gwamnan jihar ya dauka a gobe 14th gawatan Fabrairu

Yan kabilar Jonathan zasu yi gangamin kin jinin Fulani
Yan kabilar Jonathan zasu yi gangamin kin jinin Fulani

Sai dai kuma wasu shugabannin kungiyoyin da ke shirin yin zanga-zangar sun bayyana cewa da wuya su iya yin zanga-zangar saboda wani matakin da aka ce masu gwamnati ta dauka wajen kama dukkan wanda ya kuskura yayi.

KU KARANTA: Na je wurin Buhari - Hadi Sirika

Wasu daga cikin kungiyoyin da suka nuna sha'awar su da shiga gangamin sun hada da: The Niger Delta Security Watch Organisation of Nigeria (NDSWON), Ijaw People Development Initiative (IPDI), da kuma Foundation for Human Rights and Anti-Corruption Crusade (FHRACC).

A wani labarin kuma, Farfesa Jerry Gana wanda gogaggen dan siyasa ne kuma tsohon ministan yada labarai ya bayyana jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta kara karfi ba kamar da ba kuma yace a shirye suke su kwace mulki a zabe mai zuwa.

Jerry Gana yace tabbas yanzu PDP ta kara karfi musamman ma bayan da aka kafa kwamitin bin diddiki da kuma sulhu.

Tsohon ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci shugaban jam'iyyar Accord Party Senata Rasheed Ladoja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel