Zaben 2019: APC sun ce in ba Atiku ba sai rijiya

Zaben 2019: APC sun ce in ba Atiku ba sai rijiya

Wasu gungun mutane da suka hada kungiya mai suna Atiku Political Crusaders (APC) masu rajin ganin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar yayi takara a shekara ta 2019 sun kaddamar da shirin su a jihar Ogun.

Zaben 2019: APC sun ce in ba Atiku ba sai rijiya
Zaben 2019: APC sun ce in ba Atiku ba sai rijiya

Taron wanda ya samu halartar jiga-jigan yan Najeriya an gudanar da shi ne a dakin taro na Ago-Egun dake Abeokuta a karshen mako wanda Sanco Ese ya ke jagoranta.

Jagoran gungun mutanen Sanco Ese yace su basu da niyyar zama yan adawa ga gwamnati mai ci yanzu ko kadan.

KU KARANTA: An gangamin kinjinin jam'iyyar APC a Katsina

Shugaban ya cigaba da cewa su sun ga ya kamata ne su tattaro hazikai da masu ilimi a fadin Najeriya musamman ma masu irin ra'ayin shugaban wajen ganin a sake tsarin Najeriya sabanin yadda take a yanzu.

Dayake nashi jawabin, shugaban kungiyar na jihar Ogun Laja Bamigboye yace "wannan kungiyar tamu bata fito bane don tayi adawa da wannan gwamnatin na kasa ko kuma ta jiha."

A wani labarin, Farfesa Jerry Gana wanda gogaggen dan siyasa ne kuma tsohon ministan yada labarai ya bayyana jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta kara karfi ba kamar da ba kuma yace a shirye suke su kwace mulki a zabe mai zuwa.

Jerry Gana yace tabbas yanzu PDP ta kara karfi musamman ma bayan da aka kafa kwamitin bin diddiki da kuma sulhu.

Tsohon ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci shugaban jam'iyyar Accord Party Senata Rasheed Ladoja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel