An samu magidanci a mace cikin dakin Otal a Aba

An samu magidanci a mace cikin dakin Otal a Aba

An samu wani mutumi magidanci a mace cikin dakin Otal a Aba, jihar Abiya, a karshen mako.

An samu magidanci a mace cikin dakin Otal a Aba
An samu magidanci a mace cikin dakin Otal a Aba

Jaridar Sun ta bada rahoton cewa mutumin mai suna, Peter Ibekwe, ya fadawa matarsa cewa zai tafi kasuwanci garin Umuahia kafin ya bar gida. Amma a maimakon tafiya, sai ya tafi dakin Otal da ke Club 25 road, Abayi Aba a karamar hukumar Osisioma.

KU KARANTA: Akalla mutane 20 sun hallaka a rikici tsakanin Akwa Ibom da Cross Riba

Mutumin wanda mazaunin Ogbor Hill ne a garin ya shiga dakin Otal din da karfe 7:30 na dare, amma aka ganshi a mace da safe. An gano gawarsa ne lokacin da masu shara suka zo sharan dakin da safe amma babu wanda ya amsa.

“Bayan anyi kokarin sanar da shi, sai ma’aikatan Otal din suka bude kofan da karfi sai dai suka ga gawarshi Mr. Ibekwe. Masu dakin Otal din suka sanar da yan sanda game da abinda ya faru. Kana kuma an sanar da iyalinsa kafin aka kaisa dakin ajiye gawawwaki.” Wata majiya ta fadawa Sun.

Wata majiya tace an samu kudi N200,000 a jikinsa. Har yanzu dai ba’a samu rahoton dalilin mutuwarsa ba amma za’a gudanar sa bincike akan dalilin mutuwarsa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel